Daga Pauline Odhiambo
Dan Orenge yana ɗan shekara takwas muryarsa ta fara fashewa. Hakan ya ba da mamaki, ganin shekarunsa ba su kai na yadda aka saba gani ba, kuma hakan ya masa bambarakwai a zahiri da kuma a ɓoye.
Sai dai shi Dan bai san cewa muryarsa ba sauya kawai ta yi, za ta yi fuffuke ta kai shi wata duniyar da za ta zamo masa kadara.
Dan, wanda ake wa laƙabi da D_man, yanzu yana da shekaru 40 kuma yana da baiwar murya mai rauji da mutane ke kallo a matsayin ta musamman.
A matsayinsa na mai fasahar murya da ya cim ma nasarori, kuma mai horar da mutane kan magana gaban jama'a, yana da baiwar auna lafazi da isar da saƙo ta hanyar ƙwarewa da iya zamantakewa.
"Shigata harkar kwaikwayon murya ta fara ne shekara 20 baya, amma na samu shuhura ne bayan na fita daga rayuwa cikin maye," Dan ya faɗa wa TRT Afrika lokacin da ya yaƙi halayyar shan barasa.
"Ina yawan bayar da samfurin muryata ga kamfanonin shirya fim, kuma na je gidajen talabijin da rediyo don yin gwajin ɗaukar aiki, amma ban samu nasara ba."
Ƙoƙarin Dan na shawo kan matsalar halayya ita ta ba shi jimirin jure wahala a rayuwarsa ta aiki.
Ƙarfin halinsa ya zo daga baya, kuma ya samar masa da nasarori cikin shekaru, inda bidiyonsa a TikTok da wasu shafukan sadarwa suke samun shuhura.
Nasarori
Talla na farko na talabijin da Dan ya yi, ya zo ne cikin wata guda da fara aiki a sutudiyon abokinsa na naɗar murya.
Ya bayyana cewa, "Na samu labarin ne ranar bikin haihuwata, kuma hakan ya zamo min babbar kyauta. A ƙarshe sun yi amfani da muryata a talla guda biyu mabambanta, don haka aka biya ni ninki biyu".
Daga nan Dan ya kafa kamfaninsa mai suna Sikika Advertising Solutions. Sunan ya samo asali ne daga kalmar "sikika" ta Kiswahili, mai nufin "a ji ka".
Baya ga fasahar murya, kamfanin ya ƙware kan shirya fim ɗin motsin zane, da rubutun labari, da shirya waƙa, da ɗaukan bidiyo, da tacewa.
Dan ya ci gaba da aiki tare da tsohon ma'aikacinsa a matsayin ejan, sannan daga nan ya samu aikin zama mai gabatarwa a wani bikin ba da kyautuka.
Ya ci gaba da aikin naɗar murya a tallace-tallace. Bidiyonsa na farko da ya yi fice an nuna shi yana karanta tallan Mercedes da Range Rovers a TikTok.
"A baya ba shi da mabiya, amma a yanzu ya samu mabiya 30,000 a wata guda, wanda ke nufin samun ƙarin kuɗin shiga na kasuwanci," in ji shi.
Dan yana da 'ya'ya biyar, kuma a baya-bayan nan ya saka baki don taya masu zanga-zangar adawa da ƙarin haraji, wadda ta gudana a Kenya.
Ya faɗa wa TRT Afrika cewa, "Farin jini da nake ci gaba da samu ya sa na shiga ƙungiyar Gamayyar Masu Fasahar Murya ta Kenya, inda na samu damar gamuwa da kuma aiki tare da wasu ƙwararru".
Muryar goyon baya
Baya ga ayyukansa na tallace-tallace, Dan ya fara shirin wayar da kai kan lafiyar ƙwaƙwalwa.
Dan yana halartar shirin murya na podcast da sauran dandalin da ke magana kan walwalar ɗan-adam.
Ya ƙara da cewa, "Samun damar amfani da muryata don taimakon mutane ya tallafa min wajen mayar da hankali kan ƙoƙarina na daina komawa shan barasa".
"Ina godiya ga Allah kan cewa cigaban da na samu zuwa yanzu ya dace da abubuwan da nake muradi, ciki har da motsa-jiki da kula da lafiyar ƙwaƙwalwa."
Dan ya girma a gida da ake tsaurara tarbiyya, inda aka damu da batun karatun yaro sama da shagaltuwa ko wasa. Wannan ya sa shi ɗokin samun 'yanci irin wanda rayuwar jami'a ke bayarwa.
"Zuwa lokacin da na shiga jami'a, na sha wahala wajen daidaita karatuna da zuwa fati," inji Dan, wanda ya ƙirƙiri shafin D_Man Wellness.
"Don haka na fara motsa-jiki don na yi amfani da ƙarfin da jikina ke son sarararwa.” Ya ɗauke ni shekara biyar da rabi kafin na kammala karatun digiri, maimakon shekara huɗu".
Daga baya ya samu aiki mai ɗorewa a 2019, a wani kamfanin fasahar hada-hadar kuɗi. Cikin sa'a, aikin ya ba shi damar yin amfani da gwanintarsa ta kwaikwayon murya.
Ya kuma ce, "A lokacin ne na fara samun aikin murya da ake biya na, kuma hakan ya ƙayatar da ni saboda na samu damar naɗar bidiyon koyar da fasahar murya, da kuma sauran abubuwan koyarwa".
Ranar da ya bayyana wa maigidansa matsalolinsa lokacin da ya gaza halartar wani muhimmin taro, ta zamo masa babban sauyi a rayuwa.
"Bayyanawar da na yi ta sa na rasa aikina, amma mai gidana ya ce kamfanin zai sake ɗauka ta aiki idan na nemi tallafin likita, kuma na kawo shaidar cewa na fara karɓar magani. Kuma hakan na yi".
Tsohon mai gidan Dan ya cika alƙawarinsa, bayan ganin ya fara ƙoƙarin kyautata rayuwarsa.
"Na yi masa wasu shirye-shiryen murya, kuma sai aka aika wa matata kuɗin aikina," in ji Dan.
A lokacin ne Dan ya samu yaƙinin cewa ruhinsa ya kuɓuta daga matsalolin halayya marasa amfani.