Burna Boy da Davido da kuma Wizkid dukka sun samu manyan lambobin yabo na masana'antar wakoƙi, suna da biliyoyin adadi na wakokinsu da aka saurara da kuma miliyoyin mabiya. /Hoto: TRT Afrika  

Daga Brian Okoth

A wani gasa da ya hada Davido, da Wizkid, da kuma Burna Boy ba kawai zai janyo rarrabuwar kawuna a kafafen intanet ba, har ma a gidajen da dama a yawancin sassan Afirka, ko ma duniya baki ɗaya.

Mawaƙan - waɗanda manyan tauraru ne a fagen wakoƙin zamanı daga Nijeriya - sun kafa tarihi ta hanyar cika adadin jama'ar da ake buƙata a wuraren taro,sannan sun samu duk wani lambar yabo a fannin ƙida da waƙa. To amma, wanene daga cikinsu ya fi wani?

Tambaya ce da ba a taɓa samu, kuma da wuya a taba samun wani sahihin amsa a nan kusa.

Saboda Davido da Wizkid da kuma Burna Boy baki ɗayansu suna da lambobin da kasancewa da kuma hazakar da za su iya ɗaukan matsayi na ɗaya kowanensu.

Lambobin yabo na waƙoƙi

Burna Boy ya rera waƙoƙinsa a wurin taro na Coachella Valley Music & Arts Festival a Indio da ke birnin California, Amurka a watan  Afrilu 21, 2023. REUTERS/Aude Guerrucci

Wizkid - wanda ke da aƙalla lambobin yabo 88 a fegen sana'arsa - shi ne ya fi samun wannan ƙyauta a cikin mawaƙan uku.

A shekarar 2021, mawaƙin mai shekaru 34 ya hada kyatukan da ya samu da na Grammy. Ya lashe kyautar ne tare da mawaƙiyar Amurka Beyonce a fagen nau'in waƙar bidiyon da ya fi fice, a wakarsu mai taken "Brown Skin Girl.''

A lambobin yabon da ya samu guda 61, Burna Boya yana matsayi na biyu. Mawaƙin mai shekaru 33 ya yi ta neman samun ƙyautar Grammy wanda ya lashe a shekarar 2021 a ƙunɗin waƙoƙinsa mai suna ''Twice as Tall''. ƙundin ya lashe lambar yabo na duniya a fagen ƙunɗin wakoki.

Davido mai shekaru 31 ya na matsayi na uku, inda ya lashe kyaututtuka 32, ciki har da BET Awards, da MTV Africa Music Awards, da Channel O Music Video Awards da dai sauransu.

Wizkid ya lashe lambobin yabo har 88, cikin har da Grammy Awards. Hoto: Wizkid/instagram

Waƙoƙin da aka fi saurara

A manyan manhajoji huɗu na wallafa waƙoƙin murya da bidiyo wato Youtube da Spotify da Audiomack da kuma Boomplay — Burna Boya yana da adadi yafi yawa na wakokinsa da aka saurara, indaya kai sau biliyan 11.9.

Yawancin waƙoƙinsa da aka fi saurara suna kan manhajar Spotify inda suka kai biliyan 6.6, sai kuma YouTube da ke da biliyan 2.5.

Daga cikin waƙoƙinsa baki ɗaya, ''Location''- wanda ya rera tare da mawaƙin Birtaniya Santan Dave- yana da adadi mafi yawa da aka saurara da kusan sau miliyan 572 a kan Spotify.

Wizkid ne na biyu, inda aka saurari waƙoƙinsa sau biliyan 9.5 a kan manhajojin guda hudu. A Spotify an saurarin waƙoƙinsa sau biliyan 7, sai kuma a YouTube sau biliyan 1.4.

Waƙar nan mai suna "One Dance'', wanda mawaƙin Amurka Drake ya fito da Wizkid, ya sa an saurari wakokin Wizkid kusan sau biliyan 3.4 akan Spotify.

Davido na a matsayin na uku, inda jimillar wakokinsa da aka saurara ya kai sau biliyan 5.5 a manyan manhajoji guda hudu.

A kan Spotify, an saurari waƙar Davido sau biliyan 2.1, a kan YouTube kuma a kalli waƙoƙin bidiyonsa sau biliyan 1.9.

A cikin waƙoƙinsa baki ɗaya, wakar "Fall" ita ce kan gaba inda aka saurare ta kusan sau miliyan 293 akan YouTube.

Mawaƙi kuma mai rubuta wakoki ɗan asalin Amurka da Nijeriya, Davido yana rera wakokinsa a yayin taron ba da lambobin yabo na BET a Los Angeles, a ranar 25 na watan Yuni 2023./ Hoto: AFP

Kafofin sada zumunta

A kafofin sada zumunta, Davido sarki ne. Yana da haɗa kusan mabiya miliyan 57 a kan Facebook, da kafar X, da Instagram da kuma TikTok.

A shafinsa na instagram yana da kusan mabiya miliyan 30, sai a shafinsa na X da yake da mabiya miliyan 16.

Daga Davido sai kuma Burna Boy, wanda ke da mabiya kusan mutum miliyan 43 a dukka manyan shafukan sada zumuntan guda hudu.

A shafinsa na Instagram, Burna Boy yana da mabiya kusan mutum miliyan 18, sannan a shafin X yana da kusan mabiya miliyan 10.

Shi kuma Wizkid jimillar mabiyansa da ya haɗa daga kafofin hudu ya kusan kai mutum miliyan 41. A shafin Instagram kuma yana mabiya sama da miliyan 18, sai a shafin X inda yake da kusan miliyan 14.

Don haka, wanene daga cikin ukun ya cancanci a ba shi matsayin babban sarkin Afrobeats?

TRT Afrika