Daga Pauline Odhiambo
Duk yadda mutum ya yi tunanin yadda ake fadada tunani wajen kirkira, zai yi wahalar gaske a yi tunanin za a iya amfani da itaciyar ayaba wajen hada gashi. Amma kasancewar dan Adam da basira, kullum wasu sababbain kirkire-kirkire kara fitowa suke yi.
’Yar kasuwar kasar Uganda, Juliet Tumusiime, ta zo da wani sabon salo, inda ta hada gashi ta hanyar amfani da na’ukan itaciyar ayaba da suke da su a Uganda a madadin gashin roba da aka saba da shi, wanda tuni ya samu karbuwa tare da faranta ran dubban kwastomomi.
“Tunanin ya zo min ne bayan gajiya da na yi da amfani da na’ukan gashi da dama da nake amfani da su, “inji ta a tattaunawarta da TRT Afrika.
“Kamar kowace mace, nakan yi fama da kaikayin kai da da zafi a duk lokacin da nake amfani da gashin roba.”
Juliet ta yanke shawarar amfani da na’ukan ayaba hudu ne daga cikin na’uka 1,000 da aka sani a duniya a shekarar 2015.
Bayan dogon nazari a kan yadda za ta mayar da jikin ayabar wanda asali yana da karfi zuwa silin gashi, sai ta fara aikin gwaji, wanda ya dauke ta kusan shekara uku kafin ta cimma nasara.
Kamfanin Juliet mai suna Cheveux Organique, wanda a takaice ke nufin gashin ainihi- yanzu ya samu karbuwa a kasashen Afrika da ma wasu kasashen duniya.
Tunanin kasuwanci
Juliet ta kasance tana aiki ne a matsayin manajar kula da aikace-aikace a Uganda lokacin da aka ba ta aikin gudanar da bincike a kan ayaba.
“Muna bincike ne domin samar da na’ukan ayaba wadanda sauyin yanayi da kwari ba za su iya lalata su ba,” inji ta a game da binciken nata, wanda a karshensa suka kuma samar da garin ayaba.
Bayan ta kammala binciken, sai kuma batun nemo manoma da za su fara noma wannan irin na ayaba da suka gano.
Sai dai wannan bai zo mata da kalubale ba, kasancewar Juliet ta taso ne a yankin da kusan kowa manomin ayaba ne.
Sai dai bayan an yanke ayabar, sanda ko jikin ayabar zubarwa ake yi, ko kuma a mayar da shi maganin kashe na’ukan ganyayaki da ba a bukata a lambu.
“Wannan ne ya tuna min yadda muke amfani da jikin ayabar wajen hada ’yar tsana lokacin muna yara. A lokacin ne sai na fara tunani wane abu zan iya yi wanda zai zama mai amfani,” inji Juliet.
Nan sai ta shiga bincike mai zurfi, inda a karshe ta gano ana amfani da itaciyar wajen hada yaduka a Indiya da Philippines.
“Sai na kara zurfafa bincike a kan shin wai yaya suke yi? da na gano, sai na ga to ai kamar za a iya mayar da shi silin gashi,” in ji Juliet.
Kawo sauyi
Da ta ga lallai akwai alamar nasara, sai ta nemi shawarar masana kimiyya.
“Ba mu da injin da zai yi yayyanka jikin itaciyar a Uganda, muna dai ganinsu a yankin Asiya. Sai muka fara amfani da hannunmu wajen bare shi sala-sala.
“Bayan mun bare, sai muka ga wani farin sili a ciki, wanda bayan mun busar, sai ya kara yin kyau sosai musamman bayan an kitsa shi a kan wata ’yar tsana.”
Amma kuma sai ya kasance gashin yana da karfi ta yadda ba zai yiwu a tankwara shi wajen yin kwalliya ba idan ana kitso, wanda hakan ya sa Juliet da ma’aikatanta suka fara tunanin yadda za a mayar da shi mai laushi.
“Da muka dukufa, sai muka samu nasarar mayar da shi mai laushi, inda muka fitar da kammalallen gashin na farko a shekarar 2018, wanda kuma za a iya rinawa, kuma a kitsa shi,” inji ’yar kasuwar.
Bayan shekara shida da farawa, yanzu ta fi samun kwastomomi daga kasashen Sweden da Amurka da Birtaniya, inda kwastomomin suke kaunar gashin saboda yadda yake narkewa a cikin kasa idan an gama amfani da shi an zubar.
“Ba ya jawo kaikayi, sannan za a iya sake amfani da shi har sau uku,” inji Juliet a game da gashin, wanda ta ce ta samu sahalewar kwararrun likitocin fata, da masana bangaren kula da gashi da sauransu.
“Mutane da dama ba su da masaniyar cewa gashin roba da suke amfani da shi da robar ba da a iya sake amfani da ita ake hada su, sannan kuma suna da illa ga muhalli,” in ji ta.
“Amma mu gashinmu na ayaba, ya zo da sauyi. Bayan an gama amfani da shi, idan aka zubar, zai narke a cikin kasa a cikin ’yan makonni.”
Kamfaninta yana sana’anta kusan kilo 5 na gashin ayaba duk wata. Yanzu haka farashin gashin ya kai Dalar Amurka 50 a kan duk giram 150, wanda hakan ya sa ya yi tsada ga talaka, amma kuma ya ci kudinsa ganin yadda ake iya amfani da shi, da kuma kyawunsa kamar yadda Juliet ta bayyana.
“Aikin hada gashin yana matukar cin kudi domin da hannu muke barewa,” inji Juliet, wadda take da ma’aikata kusan 20 na dindindin.
“Muna ta kokarin nemo hanyoyin saukaka aikin, domin samun damar rage farashin gashin ta yadda mutane da dama za su mallake shi.”
Sake amfani da shi
Domin kare gashin daga tattarewa, Juliet ta ba da shawara a kiyaye gashin daga tara danshi, kasancewar za a iya wanke shi, a shanya shi a kitse. Amma tattara shi ta baya yana hana danshin taruwa.
Kamar kowane irin kasuwanci, masana’antar na fitar da datti, sai dai a kamfaninta, Juliet da ma’aikatanta suna kokarin sana’anta dattin zuwa wasu abubuwa da za a iya amfani da su, kamar kayan kwalliya na daki da sauransu.
Haka kuma tana hada gwiwa da wasu wuraren kitso da kamfanoni a Kampala domin tabbatar da ana zubar da gashi yadda ya kamata.
“Akwai wani waje a Kampala inda muke zubar da duk gashin roba da aka shigo da su daga kasashen ketare bayan an gama amfani da su,” inji Juliet.
“Ina so in wayar da kan mutane ne a kan bukatar da ke akwai na zubar da robobi da sauransu da kyau ta yadda ba za su taru su tare mana hanyoyin ruwa ba, ko kuma su kare a cikin abincinmu.”