Sylvère Boussamba ya ƙaddamar da shirin École 241 kusan shekaru biyar da suka wuce. / Hoto: TRT Afrika

Daga Firmain Eric Mbadinga

Akwai wani sanannen bidiyo na shekarar 1995, cikin wani shirin YouTube da ya nuna mai gabatar da shirin murya a Amurka David Letterman, yana nuna al'ajabi yayin da shugaban kamfanin Microsoft, Bill Gates cikin tsanaki yake masa bayanin mene ne intanet.

A wani ɓangare na bayaninsa, Letterman ya tambayi Bill Gates, "Me ya sa ba ni da kwamfuta?"

"Wani ɓangaren matsalarka shi ne kana da tarin mataimaka," in ji Bill Gates.

Idan muka dawo yau shekarar 2024, shi ma matashi masanin fasaha, Sylvère Boussamba yana aiki kusan duka rana don koyar da fasahar dijital ga ɗalibai yara da manya, a kasarsa ta haihuwa, Gabon.

Yana da burin horar da mutane 100,000 a taƙaitaccen lokaci, domin su iya shiga harkokin sana'a da ke buƙatar ƙwarewa kan cigaban intanet da kasuwancin dijital, da sauransu.

Kusan za a ce Boussamba shi ya koya wa kansa duka iliminsa, tun lokacin da ya fara harkar shirin kwamfuta sanda yake shekara 11. A ɓangarori da dama, ya kasance yaro ne da ya taso ana tsaka da sauyin da Gates yake ƙoƙarin yi wa Letterman jawabi ƙasa da shekaru 30 baya.

Neman cimma burin 2034

Tun 2018, lokacin da Boussamba ya ƙaddamar da shirin École 241 a birnin Libreville, horar da matasan Gabon ƙwarewa a ayyukan dijital ya zamo manufarsa.

Sai dai kuma, don faɗaɗa manufofin shirin, ya fito da zaɓin yin karatu ta kan-layi ko a cikin aji, sannan ya ƙara kalmar "Al'ummomi" a sunan shirin nasa.

A matsakaicin lokaci, shirin École 241 Communities yana fatan tallafa wa aƙalla 'yan Gabon miliyan guda, wanda a yanzu ya kai rabin al'ummar ƙasar, don su fahimta kuma su ƙware kan asalin dabarun dijital nan da shekarar 2034.

Abin da mai samun horo ke buƙata kaɗai shi ne babbar waya, kwamfutar hannu, ko kwamfuta, sai kuma sha'awar samun ƙwarewa a fasahar dijital, da gina intanet, ko kasuwancin intanet cikin taƙaitaccen lokaci.

Boussamba da tawagarsa sun ƙirƙiri kundin darussan fara koyon ƙwarewa a dijital, don masu koyo da ba za su iya biyan kuɗin karatun sana'a ba.

Venceslas Bybaya Moussounda, ɗaya daga cikin waɗanda suka ci moriyar shirin, ta faɗa wa TRT Afrika cewa, "Kafin shirin École 241, ina da masaniya kan harkar, amma ba ni da ƙwarewa."

"Na zaɓi na samu horon zama masanin dijital, wanda tamkar kayan aikina ne. Tsarin shi ne mutum ya zamo mai ƙwarewa kala-kala, yadda zai iya amsa duka buƙata. Zai iya zama mai zayyana, mai zane, ko manaja."

Ɗaukakar harkar dijitala a Afirka, ta haifar da samuwar cibiyoyin harkar kwamfuta, waɗanda ke tasowa a faɗin nahiyar. / Hoto: Reuters

Bayan samun horo da ƙwarewa na watanni takwas, za a yaye matashin daga zama mataimakin manaja a kamfani mai zaman kansa, sai ya koma manaja.

Moussounda, wanda ya samu horo a kyauta, ya kammala da satifiket da kuma shaidar da ke bunƙasa damarsa ta samun aiki a gaba.

Ita ma wata 'yar Gabon, Syntiche Jisca Esseng Oyono, ta shiga shirin samun horon da ya gabaci shirin École 241 Communities, lokacin da take karatun jami'a a Libreville. Bayan shekara biyar, yanzu tana jagorantar wani shiri na sayar da inshora ta banki.

Ta ce, "Cigaban da na samu a aikina kusan kacokan sanadiyyar ƙwarewar dijital ne, wadda na samu ta hanyar shirin".

Shirin École 241 Communities na samar da horo kyauta wanda ya haɗa da darasi kan kasuwancin intanet. Yana samar wa ɗalibai dabarun amfani da wayoyinsu don gudanar da aiki, da kammala ayyukan gudanarwa, da iya aiki da manhajoji.

Cigaban dijital mai wahala

A cewar hasashe daga Boston Consulting Group, tattalin arziƙin Afirka fannin dijital zai kai darajar dalar Amurka miliyan $180 nan da shekarar 2025, da kuma biliyan $712 nan da 2050.

Tuni nahiyar Afirka ta samu cigaba wajen ƙirƙirar zaurukan gina harkokin intanet a fannoni kamar hada-hadar kuɗi ta dijital, kiwon lafiya ta intanet, da kasuwanci ta intanet.

Kusan kashi 87% na manyan 'yan kasuwar Afirka sun gano cigaba a fannin ƙwarewar kwamfuta batu ne mai fifiko da ke buƙatar ƙarin zuba jari.

Boussamba, wanda kuma babban masanin gudanar da harkar Fasahar Sadarwa ne, ya yi imanin cewa wannan kyakkyawan lokaci ne da nahiyar Afirka za ta saka ƙaimi.

"Don cimma buƙatun ayyukan dijital a nahiyar, dole a horar da ma'aikata miliyan 650 su samu ƙwarewa nan da 2030. Idan muna so mu inganta yaɗuwar harkokin dijital a Gabon, muna buƙatar horar da al'ummarmu a babban mataki." Boussamba ya sanar da TRT Afrika.

A cewar UNESCO, a Afirka kashi 11% kacal na waɗanda suka kammala karatu a manyan makarantu ne suke da horo kan dijital. Hukumar ta MDD ta yi nuni da saurin watsuwar intanet tsakanin gidaje da ya tsaya a matakin 11%, idan an kwatanta da kusan kashi 36% a ƙasashen Larabawa.

Yayin da kashi 28% na gidaje a ƙasashe masu tasowa suke da na'ura mai ƙwaƙwalwa, a ƙasashen da ke kudu da Sahara matakin ya tsaya a kashi 8% kacal.

TRT Afrika