Daga Firmain Eric Mbadinga
Tsarin amfani da filaye da kasa a Gabon na 1930 ya bayyana dazukan kasar a matsayin yankuna masu daraja da z asu zama mahangar kowanne cigaba.
Libreville, babban birnin Gabon, a wancan lokacin na da dazuka hudu da suke kawata birnin da kuma biyan bukatar muhallan yankin.
Bayan shekaru da dama, uku daga cikin wadannan dazukan sun zama wajen bayar da alkaluma kawai. A wajen da a baya ake da rumfunan zama na korran ciyayi, layukan gidaje da sauran gine-ginen cigaba sun zama magadan wannan waje a cikin mummunan yanayi.
Dajin Livrebille da ke raye a yanzu, Sibang Arboretum, kamar shi ma yana kan hanyar tafiya. A yayin da jaruman kare muhalli na Gabon ke gwagwarmayar kubutar da dajin daga bacewa, abin ya zama kamar kishirwar rusa dazukan ta ki gushewa.
Fifikon ayyukan da ke cin karo da juna
Mai fafutukar kare muhalli Francois Boussamba na hasashen mummunar makoma ga Libreville idan har Sibang ya kare kamar sauran dazukan uku wanda a tsakaninsu ne aka samar da birnin.
Ya fada wa TRT Afirka cewa "Tsuntsayen da suke yin sheka a nan ba sa samun wajen yin gidan nasu. A baya namun dawa na zuwa nan wajen su koma. A yanzu dabbobin nan ba su da wajen ɓuya. Za mu iya wayar gari wata rana."
Hektare 16 na Sibang waje ne da ke dauke da tsirrai 170 da a yanzu ake tsoron na iya bace wa wadanda su ke bayyana yawaitar arzikin halittu na Gabon.
Gudunmawar da wannan daji ke bayarwa ita ce ta samar da iskar da ake shaƙa mai inganci. Nau'ikan bishiyu daban-daban, ciki har da tsofaffin bishiyun kuka, sun zama kamar tafkunan iskar carbon, suna zuke carbon dioxide daga duniya suna ajiye su a jikinsu.
Dajin areboretum kuma waje ne da ya tattara Okoume, wani nau'in bishiya na Gabon, da kuma ciyawar Amorphophallus.
A birni kamar Libreville, garin da ke dauke da kashi 50 na al'ummar Gabon, wanzuwar arboretum tun 1954 ya zama babban jigon hana kwararowar hamada.
Yawaitar raee bishiyu
Christopher Abaga, wani kafinta kuma mai sna'ar sare bishiyu, na yawan ziyartar arboretum don kwaso abubuwan da ya kira matattun katako.
Ya shaida wa TRT Afirka cewa "Mun san an hana sare bishiyu a wanan dajin. Saboda haka, muna jiran duk wata dama ta amfani da bishiyun da suka fadi da kansu."
Charlie Abessolo, wanda ke zaune a kusa da dajin, shi ma na yawan zuwa dajin. "Wadannan rassan da na tattaro na da amfani wajen maganin ciwon hakori. Kanwata tana da ciwon haƙori, shi ya sa na je daji da safe don samo magani," in ji shi.
Mai fafutuka Boussamba da abokan aikinsa na ta aiki ba gajiyawa don hana sake sare daji daya tilo da ya rage wa Libreville.
"Mun fara ayyuka da dama da manufofi masu hawa biyu - mu ga matasa sun bi sahun mu don ci gaba da wayar da kan jama'a kan bukatar kubutar da wannan daji," in ji shi.
"Wannan dajin na arboretum ba tantama shi ne cibiyar wayar da kai game da dazuka, da ke kasar tsakiyar Afirka da ke da dazuka mafi yawa da girma a nahiyar."
Gwagwarmayar kare dazuka
Alpha Marah, wadda ta jagoranci sashen bayar da kariya ga dajin karkashin wata kungiya mai zaman kanta ta La Lowe, ta kasance a kan gaba wajen kokarin ganin an hana sace wa da rushe wannan daji."
Marah tells TRT Afrika. Marah ta fada wa TRT Afirka cewa "Muhimmancin kare Sibang ya haura muhimmancin wata bukata ta cikin gida ko ta tattalin arzikin wadanda ke rusa shi. Muna bukatar daukar wannan mataki cikin gaggawa."
"A yanzu dai, mun shiga ayyukan bayar da shawaram bayar da horo da aikin kwararru a dukkan fadin kasar. Muna neman masu bayar da gudunmowa da z asu tallafa wa kokarin Gabon na kare muhallinsu.
"Muna aiki don tabbatar da cewa an inga wanzuwar itatuwa daban-daban don amfanin al'ummu masu zuwa."
Tun samun 'yancin Gabon a 1960, cibiyar 'Institut de Recherches Agronomiques et Forestières of de Pharmacopoeia da Traditional Medicine' ce ke kula da arboretum, dukkan su hukumomi ne da ke karkashin ma'aikatar binciken kimiyya.
Henri Bourobou, daraktan cibiyar magungunar gargajiya, ya yi amanna cewar ba tare da samar da madadin katakon timber ba, zai yi wahala a kawo karshen sare bishiyu a Sibang.
"Sibang na kewaye da unguwannin da mazaunansu ke sare shi. Wannan abu ne mai wahala." Bourobou ya fada wa TRT Afirka.
Rashin kariya ga dazuka
Mongabay, kungiyar kasa da kasa mai kare muhalli, ta bayar da rahoton cewa Gabon na rasa sama da hekta 10,000 na dazuka kowacce shekara saboda sare bishiyun.
Ghisiain Moussavou na sashen kare dabbobin dawa a ma'aikatar ruwa da gandun daji ta Gabon ya gano muhimmancin hada kai da kungiyoyi na cikin gida abokan aiki masu zaman kansu don kare dazuka irin su Sibang Arboretum.
Tun shekarar 2002, Gabon ta sadaukar a kashi 11 na iyakokinta ga kare muhalli inda ta kuma kara yawan filaye shakatawa na kasa daga guda bakwai zuwa ashirin.
Nazari da dama da aka gudanar sun bayyana kusan kashi 20 na tsirran da suke Gabon babu su a wani yanki na duniya.
Wasu daga wadannan tsirrai 'yan tsiraru na daga cikin bishiyu 170 d ake dajin Sibang Arboretum.