Daga Emmanuel Onyango
A yayin taron ranar Laraba na shugabannin kasashen Gabashin Afirka kan rikicin Jumhuriyar Dimokuradiyyar Kongo, ba a samu cim ma wata matsaya mai ma'ana ba da za ta kai ga warware rikicin.
Shugaban Kasar Kongo Felix Tshisekedi ya kaurace wa taron na yankin. Takwaransa na Rwanda Paul Kagame ya fita daga taron da wuri, wanda ke bayyana salon alakar da ke tsakanin kasashen biyu makota.
Tabarbarewar rikici a Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo ya tsugunar da fararen hula 400,000 a watan da ya gabata kaɗai. Wannan kari ne kan mutane fiye da miliyan bakwai da aka raba da gidajensu a 'yan shekarun nan, kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana.
An fara rikicin a 1990 inda 'yan kungiyoyin bindiga da dama ke yaki da dakarun gwamnati da na kasashen waje da ke wanzar da zaman lafiya.
Rikicin ya dauki shekaru da dama. Haka kuma ya gagari warwaruwa a matakin kasa, yanki da kasa da kasa. Matsalolin rikicin sun ta'allaka ne ga gyauron kisan kiyashin Rwanda a 1994, gami da dalilan tsaro da na tattalin arziki.
Yankin na ɗauke da muhimman albarkatun kasa na 'tantalum' a 'coltan' wadanda na da amfani sosai wajen samar da batiri. Amma kuma ba sa amfanar jama'ar yankin sosai. Kwararrun Majalisar Dinkin Duniya sun ce ana kasuwancin albarkatun ta haramtacciyar hanya ta kasar Rwanda, ikirarin da Kigali ta musanta.
Shugaba Kagame ya nace kan cewa yana da muhimmanci a warware rikicin.
Kigali ta sha yawan ambata da dora laifi kan 'yan tawayen Hutu da ke da hannu a kisan kiyashin 1994 kan Tutsi a Rwanda. Sun yi amanna cewa wasu daga cikin su sun tsallaka zuwa Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo bayan kisan kiyashin don kafa kungiyar Dakarun Dimokuradiyya Don 'Yantar da Rwanda, wadda ke kai hare-hare kan Tutsi da ke Kongo.
Kungiyar 'yan tawaye ta M23, wadda ta kwace yankuna da dama a rikicin baya-bayan nan, na ikirarin kare martabar tutsi da ke Kongo. Mafi yawan mayakanta sun fito ne daga lardin Kivu ta Arewa, da ke da iyaka da Rwanda.
Gwamnatin Jumhuriyar Dimokuradiyyar Kongo da Majalisar Dinkin Duniya na yawan zargar Rwanda da goyon bayan 'yan tawayen, ciki har da ba su makamai da horo. Amma Kigali ta musanta zarge-zargen.
"M23 ba 'yan kasar Rwanda ba ne," kamar yadda Kagame ya fada wa shugabannin Kasashen Gabashin Afirka a ranar Laraba. "Duk abin da za mu fada da duk abin da muka kudiri aikatawa, ya zama dole mu kalli batun yadda yake sannan sai mu ci gaba a kan haka, watakila ta haka ne za mu iya kaiwa ga gaci," kamar yadda ya kara fada.
"Idan ba haka ba kuma, ban ga ta hanyar da za a bayar da gudunmowa don warware rikicin ba."
Takwarorinsa a wajen taron na Kasashen Gabashin Afirka sun bayyana ra'ayi irin nasa inda suka yi kira ga Shugaban Kongo Tshisekedi da ya " ya yi tattaunawa ta kai tsaye da suk masu ruwa da tsaki, ciki har da M23 da sauran kungiyoyi da ke dauke da makamai da suke da damuwa".
Shirin tattaunawar da aka yi tsakanin gwamnatin Kongo da M23 da aka yi a baya bai yi nasara ba.
A don haka ba abin mamaki bane awanni bayan taron, Tshisekedi ya fito ya bayyana nuna rashin amincewa da duk wani shirin sabuwar tattaunawa , inda ya yi alkawarin fara kai manyan farmakai kan 'yan tawayen tare da kwato yankunan da suka mamaye garin Goma na gabashin kasar a farkon wannan makon.
Ya kuma soki "halin ko in kula" na kasashen duniya a yanayin tabarbarewar tsaron".
Kungiyar Kasashen Kudancin Afirka ma na shirin gudanar da taro game da halin tsaro a gabashin Kongo. Akalla dakarunsu 17 na wanzar da zaman lafiya ne aka kashe a makon nan a aranagamar da suka yi da 'yan tawaye. Mafi yawan wadanda aka kashe sojojin Afirka ta Kudu ne.
Shugaban Kasar Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya yi kira da a girmama darajar iyakokin kasar Kongo.
Shugaban kasar Angola Joao Lourenco, wanda shi ne mai shiga tsakani na Tarayyar Afirka tsakanin Jumhuriyar Dimokuradiyyar Kongo da Rwanda, ya yi yi kira 'janyewar sojojin Rwanda nan da nan" daga iyakokin Kongo.
Lourenco ya bukaci da a dawo da tattaunawar zaman lafiya tare da M23 da dukkan sauran kungiyoyin masu dauke da makamai da ke iyakokin Kongo.
Tun da fari a Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya, Ministar Harkokin Wajen Kongo Theresa Kayikwanba Wagner ya ce akwai "bukatar gaggawa don daukar matkan da suka dace Kwamitin."
"Kalmomi ba za su isa ba wajen kawo wahalar da mutane ke sha da hare-haren da ake kai wa a Goma. A yanzu lokaci ne na Kwamirin Tsaro ya dauki mataki... ya isa haka," ta fada wa taron manema labarai bayan zaman Kwamitin na ranar Talata.
A yayin da ake ci gaba da neman zaman lafiya, an samu raguwar arangama a Goma a ranar Alhamis, inda rahotanni ke nuni da cewa an ga mayakan M23 da dakarun rwanda a kan tituna.
Kayan kula da lafiya na ta gwagwarmayar ganin sun kula da wadanda aka jikata, in ji kamfanin dillanci labarai na AFP.
Hukumar Samar da Abinci ta Majalisar DInkin Duniya ta bukaci kasashen duniya da Kwamitin Tsaro da su dauki matakan dakatar da rikicin.
"Mutane na bukatar hanyoyi masu tsaro, suna bukatar a bude hanyoyi, suna son kasancewa da iyalansu, suna bukatar aminci. Mafi yawan abin da suke bukata shi ne abnci." in ji mai magana da yawun Hukumar a Jumhuriyar Dimokuradiyyar Kongo, Shelley Thakrai, yayin tattaunawa da TRT Afrika.
“Muna son mu yi aikinmu a yanayi na adalci, inda za mu samu dama mara tsaiko kuma wajen da za mu yi aikin ba tare da daukar bangare ba."