Daga Firmain Eric Mbadinga
Rachel Fatuma, matashiya 'yar kasar Kongo, watakila ba don ta zage damtse ba da tuni ana mata kallon daya daga cikin matasan Jumhuriyar Dimokuradiyyar Kongo da ke neman tudun dafawa a duniyar nan.
Amma sam ba ta zama daya daga cikin wadannan ba.
A matsayin wadda ke koyon kimiyya da karsashi, wannan dalibar da ke ajin karshe a Jami'ar Ruwenzori ta Kinshasa inda take karatun Injiniyanci, a ko yaushe na kalubalantar kanta wajen cin ribar wani abu da zai kara mata karfi da burin da take da shi na fita daban a tsakanin tsaranta.
A shekaru 24 da take da shi, Rachel ta samar da hanyar samar da makamashi ta hanyar tafiya ko yin rawa a kan tayil da aka samar da abubuwa masu arha da saukin samu.
Tsarin na kan karfin takun mutane yayin da suke tafiya a kan abin da na kira tayil masu makamashi. Suna samar da makamashin lantarki a lokacin da ka yi tafiya a kai,' Rachel ta fada wa TRT Afrika.
A shekarar 2023 ne Rachel ta gabatar da nau'in farko na taile din ta da ke samar da makamashi ga masanan kimiyya.
Wannan abu da ta gabatar ya fito da shirin da dade tana aiki a kai tsawon shekaru, da kuma cika burin da take da shi tun tana yarinya karama.
Makusanta da masoyan Rachel ne suka fara ba ta taimako na farko. Mahaifinta, mahaifiya da 'yan uwanta maza da mata duk sun dinga karfafa mata gwiwa wajen kirkira da kalubalantar masu cewa ai maza ne kawai suke karatun Injiniyanci.
Babbar ilhamar yin hakan na cikin kwayoyin halitarta. Rachel ta gaji sha'awar kirkirar sabon abu daga mahaifinta, wanda injiniyan gine-gine ne.
Hugues Twaha, daya daga makusanta abokai, ta shaida yadda Rachel ta dinga gwagwarmaya zama masaniyar kimiyya tun tana yarinya karama.
"Ita da ni mun yi tafiya guda, tun daga makarantar nasire har zuwa sakandire, zuwa babbar makarantar kimiyya da fasaha ta Mahamba da ke Butembo, inda muka nazarci lantarkin masana'antu da na bai daya." in ji Hugues.
"Rachel ta dinga haskawa ta hanyar kudirinta na fita daban. Mace kwaya daya a ajin da maza suka fi yawa, ba ta taba shayin ta kirkiri wani sabon abu ba, tana gwada sabbin abubuwa, tare da kafa tarihi. Yadda take iya daukar hatsari da tunanin sabbin mafita shaida ne na irin karfin gwiwarta da kuma yadda take da sha'awar wannan fanni."
Fara tunanin kirkira
Tunanin samar da tsarin da zai bayar da lantarki ta hanyar yin tafiya ko tsalle a kan tiles ya samu ne daga fahimtar amfani da ahuwan takun tafiyar mutane don samar da makamashi, wanda tarihinsa ke koma wa zuwa ga 1983.
Touluse Metro a Faransa ya samar da abinda ake kira "piezoelectric pavement" da ke samar da lantarki daga motsin da sahuwan dan adam ke yi a kan kasa yayin tafiya.
Rachel ta bayyana cewa wannan tsari ne ya zamar mata ilhama wajen samar da nata.
Bambancin da ke tsakanin tsarin Kinsasha da na Toulouse na tattare kan yadda na Touluse ke amfani da kayan piezoelectric don samar da makamashi, inda tsarin Rachal kuma ke amfani da tsarin samar da makamashi ta hanyar fasahar lantarki da da injina.
An samar da Piezoelectricity a 1880 inda 'yan uwa Pierre da Paul-Jacques Curie suka hannu waje guda don samar da tsarin hada gishiri da gilasai - da ake hade su waje guda don su samar da makamashi.
Shekaru da dama kafin wannan lokaci, a 1817 an alakanta assasa samar da fasahar sarrafa gilasai don makamashi ga Frenchman Abbé René Just Haüy, wanda ya bayar da gudunmowa sosai ga tsarin da abubuwan da ke tattare da shi.
Tushen aikin
Tsarin Rachel na amfani da salo mai sauki.
Ta fada wa TRT Afrika cewa "Abubuwan da ke cikin tayil di na ba sa kode wa ko daukar datti, suna da sifirin, da jenerato. Makamashi daga tayil a tsarin makamashin electromechanical na amfani da sifirin wajen sauya maotsin sinadarai zuwa makamashi."
A cikin wadannan kayayyaki, ana amfani da sifirin wajen adanawa da sakin makamashin da aka samar ta hanyar tattaki a kan tayil.
"A yayin da aka matse sifirin din, yana adana makamashi mai danko. Sannan idan aka sassauta sinadaran ko suka bar wajen, sai sifirin din ya dinga sakin makamashin da ya ajje." in ji ta.
Wadanan motsi gida biyu - matsewa da kara tsayin sifirin - ne hanyoyin da ake bi don juya masamar da ke sauya sinadarai ziwa makamashin lantarki.
"Za a dinga tattara makamashin da aka samar kuma ake amfani da shi wajen kuna kayan lantarki ko aka ajje a wajen adana makamashi, kamar batiri," Rachel ta kara bayani.
Amfani da makamashin
Tare da yawan mutane kimanin miliyan 105, Jumhuriyar Dimokuradiyyar Kongo na bukatar makamashi sosai kuma yana da muhimmanci a wajen ta. Gamayyar Yanayi da Tsaftatacciyar Iska, wani shiri karkashin kulawar Majalisar Dinkin Duniya, ya bayar da rahoton cewa kasar ta Tsakiyar Afirka na da burin cim ma wannan manufar amfani da makamashi mai tsafta nan da 2030.
Wannan kusan ya zo daidai da ayyukan Rachel.
Amma wani abin ban mamaki kuma, duk da karsashi, yabo da ma bayyana a shafukan farko na jaridun kasa a lokacin gabatar da aikinta, Rachel ta ce har yanzu ba ta samu wani tallafi da zai taimaka wajen cike gibin makamashin da kasarta ke fuskanta ba.
Amma ba ta cire rai ba, ta yarda da kanta da mafarkin da take da shi, wanda shi ne na smaar da gaske ga gidajen al'ummar kasarta.
"Ina sa ran cewa wannan aiki zai samu tallafin kudade na daukar nauyi ta yadda za mu iya samar da tayil din da za su dinga samar da makamashi sakamakon takun sahun mutane da ke tafiya," in ji Rachel. "Amfani da tayil din makamashi ba shi da wani tasdiri mai illa ga muhalli. Wannan ya sanya shi zama makamashi mai tsafta d ake da ke iya aiki ya kuma zama madadin makamashin nukiliya da fitar da gurbatacciyar iskar carbon."
Ya zuwa yau, alkaluman mahukunta sun bayyana cewa kashi 10 na jama'ar kasar da faransa ta yi wa mulkin mallaka ne ke samun isasshen lantarki. Kasar ta dogara ne kan man fetur da ruwa don samar da makamashi.