A mafi yawan lokuta ana kallon macizai a matsayin dabbobi da ke da matukar hatsari. / Hoto: Kacalla

Daga Abdulwasiu Hassan

A duk wani tsoro na duniya, maciji na daga cikin manyan abubuwan da ake tsoro.

Camfe-camfe da dama da ake fadi a cikin tatsuniyoyi da kuma labarai wadanda ba daidai ba kan tarayya tsakanin macizai da mutane na daga cikin manyan dalilan da ya sa ake kallon su a matsayin wasu dabbobi masu matukar hatsari, wadanda ke sa mutum ya yi fargaba ko ya gudu ko kuma ya kai musu hari idan ya gan su.

Masarautar Machina da ke jihar Yobe a arewa maso gabashin Najeriya, nan ne inda wannan labari na maciji ya karkata.

Mazauna wannan garin, idan suka ga macizai suna kutsawa cikin gidajensu ba su kallon hakan a matsayin wata alama ta hatsari sai dai ta farin ciki. Dangantaka ce da aka gina ta bisa mutunta juna da kuma tsarin al'adu wanda ya wuce shekaru aru-aru.

Tarihin macizai a Machina

Dangantakar Machina da macizai na da alaka da wani labari na sarauta wanda ya danganci haihuwar ƴan biyu.

Mutanen garin sun bayyana cewa macizai ba su kai hari sai dai idan an yi musu barazana. / Hoto: Alhaji Bura Babagana Machina

"An taba haihuwar sarkin garin da maciji a matsayin tagwayensa. Bayan kwanaki kadan sai macijin ya tafi cikin tsaunuka bayan fadar Sarkin Machina inda ya kafa gidansa a can. Tun daga lokacin ake kallon macizai a matsayin 'yan uwan sarki," kamar yadda Kacalla Baita ya bayyana, jami'in watsa labarai na Karamar Hukumar Machina a tattaunawarsa da TRT Afrika.

Wanda abin mamaki ne kamar yadda labarin yake, amma mutanen Machina na ci gaba da dabbaka al'adar kulawa da macizai a matsayin halittu wadanda ke da jinin sarauta a tattare da su.

Idan aka ga maciji ya zo wurin wani biki a garin, ana masa maraba a matsayin bako domin shiga cikin bikin.

Idan maciji ya shiga gidan da aka yi haihuwa wata alama ce da ke nuna wani basarake ya zo yi wa jaririn da aka haifa maraba.

"A lokacin bukukuwa ko wani abu da kan tara mutane, za ku ga kanana da manyan macizai suna shiga gidan sarki ba tare da an takura musu ba. Ba su cutar da kowa. Suna yin hanyarsu jama'a su yi hanyarsu," in ji Baita.

"Ga duk wani mazaunin Machina, macizai kamar 'yan uwansa ne wanda suka girma tare," kamar yadda ya shaida wa TRT Afrika. "Haramun ne cutar da su," kamar yadda ya kara da cewa

Mutanen garin Machina sun ce suna shan maganin maciji wanda ke kare su daga cizonsa. / Alhaji Bura Babagana Machina

Mazauna garin sun tabbatar da cewa kusan kowane gida akwai macijin da yake kai masa ziyara akalla sau daya a mako, akasari ranakun Juma'a.

Amfana da juna

Irin alakar da ke tsakanin mutanen Machina da macizai ta kai ga cewa baki daga waje idan suka je garin suna daina tsoron macizai bayan sun shafe lokaci mai tsawo a garin.

"Mutane suna zuwa garinmu suna tsammanin ganin wani abu da ba a saba gani ba. A al'ada, maciji na gudun mutane. Amma musamman a cikin gidan sarauta, sun kasance daya dgaa cikin abubuwan da ke cikin harabar," in ji Babagana.

Ko da an samu cizon maciji, wanda mazauna garin na cewa ba a cika samu ba, kowa a garin na shan maganin maciji wanda masu maganin macijin na gargajiya ke hadawa.

"Ba mu samun matsalar cizon maciji a nan. Idan ma an ji wanda abu ne da ba a saba ji ba kan cewa ya sari wani, lokaci ne na damina kuma watakila a watagona da ke can wajen gari," kamar yadda Babagana ya shaida wa TRT Afrika.

Ya bayyana cewa yana tabbatar da cewa babu wani bako da yake bari hankalinsa na tashi idan ya ga maciji na tafiya.

"Ina yi wa macizan magana kan su bai wa bakona wuri domin ya sarara. Kamar bil'adama suke. Kawai dai ba za su iya magana banme. Amma suna jin abin da ake cewa," kamar yadda ya bayyana.

TRT Afrika