Daga Mazhun Idris
A lokacin da suke ƙasa-ƙasa da murya yayin addu'a a lokacin watan Ramadan, Musulmai suna tuno da ƙarin imanin da suke samu sakamakon azumi da ibadu.
Eid al-Fitr, ranar farko ta watan Shawwal wanda ke zuwa bayan watan Ramadan a kalandar Musulunci, ranar biki ce don nuna murnar gabatar da ibadu.
Karatun Ƙura'ani da ibadun da aka yi kamar sahur (abincin kafin asubahi) da buɗa-baki (lokacin shan ruwa bayan faɗuwar rana), duka waɗannan ayyukan ibada da kyautatawa da ke da alaƙa da Ramadan, tamkar makaranta ce.
A yanzu, bayan ganin watan Shawwal, lokaci ne na fara wata tafiyar. Musulmai suna tsayuwa kafaɗa-da-kafaɗa su ɗaga hannayensu suna Sallah. Suna neman gafara, da shiriya, da rahama. Sannan suna murna da zuwan Ƙaramar Sallah.
Bikin a yankuna daban-daban
Yayan da bukuwan Idi ke farawa a safiyar da ke zuwa bayan azumin ƙarshe na Ramadan, ranar idi takan bambanta a wasu lokutan bisa la'akari da lissafin yanki.
Wannan shekarar, ga ƙasashen da suka yi azumi 29, kamar Nijar a Yammacin Afirka, ranar Talata 9 ga Afrilu suka yi Idi. Amma yawancin sauran ƙasashe sun kammala azumin Ramadana 30 sanna suka yi Idi ranar Laraba 10 ga Afrilu.
Asalin kalmar "Eid" ta samu ne daga Larabci, inda ma'anarta ita ce "bikin lokaci-lokaci" ko "biki", kuma tana da asalai daga ma'anar kalmar "maimaitawa" ko "komawa".
Ɗaya cikin manyan ranakun biki a Musulunci ita ce Eid al-Fitr, wadda ke zuwa a wata na 10 a kalandar Musulunci.
Sheikh Abdullahi Abatee Abdulsalami, mataimakin babban limamin Masallacin Jami'ar Uyo a jihar Akwa Ibom a kudancin Nijeriya, ya kira ranar Eid al-Fitr da ranar farin ciki bayan kammala azumin Ramadana.
Ya faɗa wa TRT Afrika cewa, "Musulmai suna bikin ne don murnar kammala ibadar azumin watan Ramadana, wanda ginshiƙi ne na addini. Yin bankwana da watan rahama inda aka ƙauracewa abinci da rana, shi ya sa ake farin ciki na an yi ibada mai girma".
Musulmai sukan yi shiga cikin kyawawan kaya su je masallaci ko filin idi don gabatar da Sallah da sassafe cikin jam'i ƙarƙashin limamin yankinsu.
Bayan nan, bukukuwan sukan haɗa da ziyarar dangi, da tarukan jama'a da zuwa siyayya, daidai da al'adu da yanayin gari a mabambantan wurare.
Matsin arziƙi
Ba kowa ne ya samu sukunin watayawa tare da iyalai ba kamar yadda ya so a ranar wannan biki. Nezeef Ahmed, wani mazaunin babban birnin tarayyar Nijeriya, Abuja, ya ce yanayin farin ciki shi ya fi komai muhimmanci a ranar Sallah.
Ya faɗa wa TRT Afrika cewa, "Wannan Idin ya zo lokacin matsin tatalin arziƙi ga yawan mutane. Amma kamar yadda aka saba, muna godiya ga Allah".
"Muna murnar Sallah duk da matsalolin da ke akwai. Bayan da je masallaci da yarana biyu da safe, zan dawo gida na shoirya abinci saboda baƙin da za su kamwo min ziyara. Mutane za su yi biki da wasa da dariya duk da akwai matsaloli."
Amma Idi ba a ciye-ciye ya tsaya ba. Yayin da ake cika teburin cin abinci da kayayyaki maƙulashe kuma ake ta wasa da dariya, kuma ana so a yawaita yin kyauta lokacin wannan biki.
Sheikh Abdulsalami ya ƙara da cewa, "Bayar da kyauta na nuna ruhin bikin Sallah, saboda yawan kyauta yana ƙara wa bikin armashi."
Da yawan iyalai sukan yi tafiya zuwa garuruwansu na haihuwa ko ƙasashensu don yin bikin tare da danginsu da 'yan-uwansu a yanayi na taro a gida.
Kamar sauran abubuwa da ke da alaƙa da al'ada da imani, Eid al-Fitr yana zaman magamar abubuwa masu tsarki dangane da al'ada.
Barka da Sallah!