Ana kallon bayyana albashin ma'aikata a matsayin wata alama ta nuna abubuwa a bayyane. Hoto/Others

Daga Firmain Éric Mbadinga

Yadda jama’a ke nuna damuwa kan batun albashi, musamman kudin da ake biyan fitattun mutane, ya jawo babban ce-ce-ku-ce a shafukan sada zumunta inda aka fi mayar da hankali kan cewa bai kamata a ringa tambayar nawa ake biya ba.

Idan da gaske “kowane aiki na bukatar albashi”, tabbas kudin da ake biyan shugaban kasa bai kamata a bayyana shi haka ba? Ba wai a Afirka ba, amma inda akalla ba a cika bayyana albashin shugabanni ba.

Bayyana albashin shugaban kasa da kuma maganganun mutane kan hakan ana ganinsu tamkar wata hanya ce ta fito da abubuwa a bayyane.

Sakamakon yadda wasu gwamnatoci suke a kasashen Afirka da dama, neman da ake yi na yin abubuwa a bayyane ba lallai ya zama abu mai yiwuwa ba.

A kasashe da dama, babu wasu dokoki da suka bukaci shugabanni su bayyana albashinsu. Hoto/AFP

A lokuta da dama, shiru da ake yi kan na sakawa ba a waiwayar adadin kudin da shugaba yake samu a matsayin albashi – sai dai idan an yi gaban kai domin fadin albashin.

A Gabon misali, sanarwar da shugaban mulkin soji Brice Oligui Nguema ya bayar a ranar 18 ga watan Oktoba kan fitar da jabun albashinsa a lokacin mika masa mulki ya sa mutane na son neman karin bayani kan albashin shugaban kasa.

Kiyasin da babu tabbaci

Joëlle Samia Samognho, wadda ta kammala nazarin kimiyyar siyasa da ke zaune a Libreville, na ganin wani abin assha ne tambayar nawa ake biyan shugaban kasa.

“A kasarmu, ana kallon lamarin kamar neman sanin nawa babban da a gida yake samu. A kowane lamari ma, babu wani karin bayani mai yawa kan hakan,” kamar yadda ta shaida wa TRT Afrika. Jacques Matand, wanda dan jarida ne a Congo ya amince da hakan.

“Duk wata tambaya wadda ke da alaka da albashin shugaban kasa ba a cika tattaunawa a kai ba,” in ji shi.

Sakamakon babu wani karin bayani mai yawa a kan hakan, mujallar Business Inside Africa wadda ta shahara kan batutuwan kudi, ta fito da bayanai kan “shugaban kasashe biyar da suka fi daukar albashi mai tsoka a Afirka” a Agustan 2022.

Kamar yadda mujallar ta nuna, Shugaba Paul Biya na Kamaru shi ne na farko wanda ke da albashi mafi tsoka kan dala 620,976 a duk shekara.

Sa’annan sai Sarkin Maroko shi ne na biyu mai samun dala 488,604 sai kuma Shugaban Uganda Yoweri Museveni na Uganda mai samun dala 183,216 a duk shekara.

A Yammacin Afirka, Shugaban Ghana Nana Akufo-Addo na Ghana shi ne kan gaba da na Ivory Coast Alassane Ouattara su ne kan gaba masu samun dala 6,300 a duk wata.

A Senegal, Shugaba Sall wanda watanni kadan suka rage masa kan mulki, a watan Afrilun 2017 ya bayyana cewa ya fitar da doka kan cewa kada albashi ya wuce CFA miliyan 5.

Kamar Senegal wasu kasashen Afirka na ta kokari wurin ganin cewa sun fitar da albashi daya ga shugabanninsu da kuma saka hanyoyin da za a rinka abubuwa a bayyane.

A Gabon, wani rahoto da aka yi a 2018 wanda Mays Mouissi ya yi, wanda masanin tattalin arziki ne na Gabon wanda a halin yanzu shi ne yake jagorantar ma’aikatar tattalin arziki, na ganin “minista na daukar albashin akalla CFA miliyan daya a duk wata”.

Haka kuma ministocin kasa suna da alawus na musamman idan suna tafiye-tafiye a cikin Gabon da kuma waje.

Dakta Balla Doumbia, wanda malami ne kuma mai bincike wanda yake da digiri na biyu a nazarin zamantakewa, na ganin bambancin da ake da shi kan albashin shugabannin Afirka ya samo asali ne sakamakon a “kundin tsarin mulki da dama, babu labarin shugaban kasa a ciki”.

“Domin gano nawa shugaban kasa ke dauka, dole ne a kalli yadda doka ta tanada,” in ji Dakta Doumbia a tattaunawarsa da TRT Afrika. “Ana kallon shugaban kasa a matsayin wata cibiya.

A kan haka, Kokarin neman karin bayani kan albashin shugaban kasa, idan muka yi kasafin kudi, muna kallon duka abubuwan da suka kunshi ayyukan shugaban kasar.”

Babu wani mai takamaimai lisassafin albashin shugabannin kasashe da alawus dinsu. Hoto/Others

Wannan na nufin babu wata dokar kudi da ke magana kan shugaban kasa. “Abin da muke gani su ne alawus.

A shekarun 1960, bayan samun ‘yancin kai, an dora wa shugaban kasa karfi mai yawa da ba shi da iyaka.

A bangaren siyasa misali, an tanadi kudi na musamman domin shugaban ya yi yaki da barazanar waje, kuma a lokacin wannan na cikin albashin shugaban,” kamar yadda Dakta Doumbia ya bayyana.

Ya bayar da misali da Mali, inda aka rinka biyan shugabannin kasashe albashi mai yawa inda aka rinka kiran albashin da “sirrin kasa”.

“Lokacin da aka soma mulkin dimokuradiyya a Mali a 1992, dole muka soma tantance lamura. Abubuwan da ake kira sirrin kasa, wadanda suka hada da abubuwan tsaro an cire su kai tsaye daga ofishin shugabam kasa,” in ji Dakta Doumbia.

Kamar yadda malamin ya bayyana, dokar kudin wadda ta dogara kan dokar kasa, ita ta saka albashin shugaban kasa.

"Idan dokar tsarin mulki ta shugaban kasa ta ba da shawarar kari ko alawus da aka wuce gona da iri kuma hakan na iya kawo cikas ga kashe kudaden jama'a, za a iya soke wannan doka ta kwayoyin," in ji Doumbia.

Dangane da kasar da kuma kungiyoyin cikin gida, tsarin tantance albashin shugaban kasa na iya bambanta, kuma a wasu lokuta, hana jama'a masaniya, yana sakawa ana tambayoyi daban-daban.

TRT Afrika