Daga Firmain Eric Mbadinga
Farin cikin Modeste Codjo Bessanh ya yi yawa sosai. Kuma ba wai dabo kawai kasarsa ta Côte d'Ivoire ta yi ta doke Nijeriya da ci 2 da 1 a wasan karshe na gasar AFCON karo na 34 ba.
A gasar da aka fafata tare da ganin manyan kungiyoyi suna faduwa, kungiyar da ta fi kowacce yawan taɓuka abin kirki a irin wannan gasa ma ba ta kai gaci ba.
Kasuwancin Bessanh na bayar da hayar motoci a birnin kasuwanci na Côte d'Ivoire, Abidjan na daya daga cikin kasuwancin da suka samu tagomashi sosai.
AFCON da aka yi tsakanin 13 ga Janairu da 11 ga Fabrairu, ta zama babbar damar kasuwanci ga kanana da manyan 'yan kasuwa da suka dinga amfana daga alfanun kwallon kafa.
"Bessanh ya fada wa TRT Afirka cewa "AFCON ta yi kyau sosai. Na yi amanna Côte d'Ivoire na iya karbar gasar cin kofin duniya."
Ya ci gaba da cewa "Kamfanina ya bayar da hayar kusan dukkan motocin da muke da su ga 'yan jaridu da suka shigo kasar don zama a lokacin gasar. Ni dai a waje na komai ya tafi yadda ya kamata."
Bessanh da ke da kusan SUV goma da kananan motoci, ya samu tsakanin CFA 40,000 zuwa 100,000 kowacce rana daga hayar motocin.
Haka ma a sauran birane hudu da aka yi gasar, kasuwanci sun gara sosai.
Shiri na dogon lokaci
Dr AI Kitenge, masanin tattalin arziki daga Jumhuriyar Dimokuradiyyar Kongo ya ce bai kamata a auna tasirin da gasa irin AFCON za su yi kan tattalin arziki ta fuskar ribar da aka samu nan da nan ba.
Ya ce "A yayin da kasa ta nemi daukar nauyin gasar kasa da kasa, ta wasanni ko wasu bangarorin, so wani lissafi ne da ke nuni da ayyuka na musamman da dogon shirin cigaban tattalin arziki."
"Akwai samun kudade da ke zuwa tare da tantancewa, kama dakuna da zuwa gidajen abinci, da suaran su.
"Wannan na da alaka ta kai tsaye da bukatar da manyan bangarori ke da ita ga kananan masu samar da kayayyaki. Za mu iya ganin cewa alfanun na zuwa har ga can kasa."
Manyan taruka irin na AFCON na farfado da batun smaar da kayayyaki da bukata, wanda a karshe yake amfanar kasuwanni da kayayyakin kasar da ke karbar bakuncin gasa ko taro, ba tare da duba ga bangaren wasanni, tattalin arziki ko al'adu ne ba.
Fervour da kayan kamshi na gida
A Anoumabo, daya daga cikin gundumomin Abidjan da suka shara, Iliasse Dayamba ya yi amfani da damar gasar wajen sayar da abinci ga dubunnan 'yan kallo da suka zo don halartar gasar ta AFCON a Côte d'Ivoire.
Dayamba ya gano a yayin gasar cewa kudaden da aka samu a gidan sayar da abincinsa a ke Au Burkina 3, sun dogara ne kan kwazon da kungiyar kwallo ta nuna. An samu kudi sosai a lokacin da Burkina Faso da Côte d'Ivoire suna fafata wasa.
Ya fada wa TRT Afirka cewa "Mun samu masu sayen abinci daga kasashe da dama. 'Yan Côte d'Ivoire ne suka fi kowadanne yawa, amma akwai magoya bayan wasu kasashen. A ranakun buga wasa, ina samun kudade sosai, musamman a bangaren sayar da kayan sha."
Kamar sauran masu gudanar da kasuwanci, Dayamba ya san yana bukatar kara yawan damarmain da yake da su.
Ya ce "A wannan yanayi, abu mafi muhimmanci a yi shi ne a tallata da habaka kayan da ake samarwa da ayyukan da ake yi wa jama'a. Kana bukatar mayar da hankali wajen tallata yankin ta yadda mutane z asu gano darajar kadarorinsu."
Baya ga bangarorin da ke samar da ayyuka kamar irin na Bessanh da Dayamba, AFCON 2023 ya bayar da damarmaki ga kasuwanci da yawa - daga abinci zuwa kayan amfanin yau da kullum - a wajen kasuwancin da ke kusa da filayen wasannin d aake kira "Villages de la CAN".
Gwamnatin Côte d'Ivoire ta yi hasashen zuba jarin dalar Amurka $1.5 wajen karbar bakuncin gasar AFCON karo na 34, ta kashe kudaden wajen gina wa da sabunta filayen wasanni shida.
Zuba jari don amfanin gobe
Shin gina wasu manyan gine-gine don wani taro ko gasa na da amfani bayan gasa ko taron?
Dr Kitenge ya yi amanna cewa kowacce kasa na yi aikinta don ganin wannan zuba jari bai zama na lokaci kankani be, wanda za a yi kokarin ganin ya ci gaba da amfanarwa sosai baya ga biyan bukatar karbar bakuncin gasar.
Ya shaida wa TRT Afirka cewa "Misali idan kuka kalli Olympic Village da aka gina a Landan a 2012, an sayar da komai bayan gama gasar. SUn gina filin wasa na wasannin Olympics zalla, amma ta hanyar da za a iya kwance kayan a kai su wani waje don amfani da su."
"A yayin da ka samar da wasu gine-gine don amfanin gajeren lokaci, to dole ne ka yi tunanin wanne amfani za a yi da wajen a nan gaba. Kuma wannan ya dogara ne kan kokarin kowacce kasa."