Abun da binne mutane na farko da aka yi a Afirka yake fada mana game da dan adam

Abun da binne mutane na farko da aka yi a Afirka yake fada mana game da dan adam

Masana tarihin rayuwar dan adam da inda ya zauna, sun gano kabarin yaro karami, “Mtoto”, wanda aka binne shekaru 78,000 da suka gabata.

Ba a san abubuwa da dama ba game da aiyukan da ake yi kan ajje gawarwaki a Zamanin Dauri ba a Afirka, amma wannan abu ya sauya a yanzu inda masana kimiyya suka gano wani yaro da aka binne shekaru dubu 78,000 da suka gabata a bakin kogon Panga ya Saidi dake Kenya.

Nazarin da aka yi a ramin ya nuna yaro ne a ciki mai shekaru 3, wanda aka tono saboda aiki da ake yi a kogon, wanda wannan ne kabari mafi tsufa da aka samu a duniya. Masanan sun kira yaron da suna “Mtoto”, lakabin “yaro” a yaren Swahili.

Wannan abu da aka gano sakamakon bincike na tsawon lokaci ne da Cibiyar Binciken tarihin Dan Adam ta Max Planck ta Jamus ke yi tare da Gidan Adana Kayan Tarihi na Kasa na Kenya,wanda a karon farko aka fara a 2010, lokacin da aka fara haka a wajen.

Masanan kimiyyar sun gano wasu kasusuwan yaron a 2013, da kuma a 2017 lokacin da suka gano ramin. An dauki lokaci mai tsawo kafin su gano muhimmancin abun da suka tono.

“A wannan gaba, ba mu da tabbacin me muka samo. Kasusuwan sun yi kanana a ce za a yi nazari a kansu.” inji Dr. Emmanuel Ndiema na Gidan Adana Kayana Tarihi na Kasa na Kenya.

“Kawaidai mun samo abun da ya sanya mu zumudi - amma an dauki lokaci kafin mu gano muhimmancinsa”.

Bayan tono ramin, sai aka dauki kasusuwan da sauran sassan ramin zuwa Burgos, Spaniya inda Malaman Mimiyya na CENIEH suke da zama.

Darakta a Cibiyar Bincike Samuwar Dan Adam ta Kasa (CENIEH) Farfesa Maria Martinon-Torres ta bayyana cewa “Mun fara tono bangaren gaba na kokon kansa da fuska, sannan muka ga alamun hakora da muka-mukai.”

“Abun mamaki kasusuwan hakarkari da na laka duk sunan nan ba su narke a kasa ba, har sangalalin baya ma yana nan kalau, wanda ke nuna binnewa ba wadda aka yi a hargitse ba ce, saboda jikin ya narke a cikin ramin da aka samu kasusuwan.”

Sabbin bayanai game da al’adun mutanen baya

Wannan abu ba shi ne mafi tsufa a duniya ba, amma a Afirka inda dan adam ya fara bayyana.

Wajen da kan yaron yake, wanda akayi masa matashi da wani abu, na nuni da akwai yiwuwar an yi jana’izarsa ne. Cibiyar Max Planck ta bayyana cewa akwai yiwuwar a zamanin baya yara kanana ake yi wa irin wannan kwanciyar a kabari.

Wannan gano abu da aka yi na da matukar muhimmanci wajen bayar da haske kan mutane da yadda muke kula da mamatanmu, inji Cibiyar CENIEH. A bayyana yake karara, mutane a zamanin baya a Afirka suna bayar da muhimmanci ga karshen rayuwa, maimakon kawai su jefar da gawa.

Farfesa Martinon-Tırres ya shaida cewa “A lokacin da muka fara ganin halayya a inda ake da nuna sha’awar kulawa da matattu, kuma sun haura ma kayan da ake bukata don aikin kula da gawar, sannan ne muka fara ganin alamun zuci.”

“Wannan ne ya sanya wannan abu zama na musamman. Muna kallon dabi’a da ta sanya muka zama bani adam. Kuma bayyananniyar dabi’a wadda ke dabbaka alaka da matattu.”

An samu wasu turaku na dutse tare da kasusuwan dan adam- abun da masana suke tunanin na da alaka da mutanen farko. Watakila an binne mamatan ne a zamanin mutanen da suka fara kirkirar kayan fasahar kere-kere.

Ndiema ya lura da cewa “Alakar dake tsakanin binne wannan yaro da Zamanin Duwatsu na Tsakiya ta taka rawa sosai wajen nuna yadda zamanin mutanen farko yake, babu tantama, su ne suke da masana’antun samar da wadannan abubuwa.”

TRT World