An koma Ayaba: Masu sana’o’i a Yuganda na samar da jabun gashi, dardumai daga ciyayi

Ayaba tayi matukar shuhura a Yuganda. A yanzu masu sana’a sun gano za ma ta fi samun daraja sama kasancewarta amfanin gona.

A lokacin da manoma suka girbe ayaba daga bishiyunta, suna barin gangar itatuwa rassanta su motse su rube sannan su zube kasa. TexFad na daukar ganyayyakin da manoma suke jefar da su.

Kimani Muturi, Manajan Darktan kamfanin TexFad ya shaida cewa “Idan na duba na kali yadda ayaba ke girma a wannan kasa, muna samun datti da shara da dama da ake zubarwa a lambunan ayaba”.

TexFad na jarraba yin abubuwa da dama da ganyen ayaba, samar da dardumai, gashin da mata ke karin gashi da shi, inji Muturi.

Gashi yau, takin gargajiya gobe

Ya ce “Gashin da muke samar na da kyau kuma ba a zubar da shi,” “Bayan amfan da shi, matanmu na zuwa su binne shi a kasa bayan sun gama amfani da shi inda zai zamar musu taki a gonakin kayan lambunsu.”

TexFad na ta yin gwaji da kokarin ganin sun mayar da ganyen ayaban masu laushi sosai kamar auduga inda za a fara samar da tufafi da su.

A ‘yan kwanakin nan a kamfanin TexFad dake Mukono, gabas da babban birnin Kampala, matasa suka girbe bishiyar ayaba tare da cika ta a kan mashinansu.

Daga baya kuma, sai ya zamana ana samar da dogayen zarirrika inda ake snaya su a waje su bushe sanna a sarrafa su a yi dardumai.

Muturi ya yi hasashen cewa TexFad zai samar da manyan dardumai dubu 2,400 a wannan shekarar, wanda hakan ya ninka na shekarar da ta gabata. Kamfanin dake da ma’aikata 23, yasamu kusan dala dubu 41,000 a shekarar da ta gabata, wannan ne kudi mafi yawa da ya samu tun bayan kafa shi a 2013.

Kamfanin na sa ran fitar da dardumai na alfarma a karon farko a watan Yuni, zuwa ga abokan cinikayyarsa dake kasashen Amurka, Birtaniya da Kanada.

Muturi ya tunatar da haske, kayayyaki na asali za su maye gurbin wadanda aka samar da ba na asali ba, inda za a dinga samar da takardu da ma kudade da su.

Ya ce “Ganyayyakin ayaba su ne takardu da yaduka na nan gaba a ban kasa”.

Reuters