An samu ɓarkewar zazzabin dengue da cutar amai da gudawa masu tsanani waɗanda suka yi sanadiyar mutuwar ɗaruruwan mutane a ƙasar Sudan da ke fama da yaƙin basasa, a cewar ma'aikatar lafiya ta ƙasar a ranar Litinin.
Ma'aikatar ta yi gargadin cewa "mummunan bala'in" na iya mamaye tsarin kiwon lafiyar ƙasar baki ɗaya.
A wata sanarwa da ta fitar, ƙungiyar likitoci ta Sudan ta yi gargaɗin cewa yanayin kiwon lafiya a jihar Gedaref da ke kudu maso gabashin kasar, da ke kan iyaka da kasar Habasha, "yana ƙara taɓarɓarewa cikin wani mummunan yanayi", inda dubban mutane suka kamu da zazzabin dengue.
Duk da cewa jihar ta Gedaref ta tsira daga mummunan sakamakon yaƙin da ake gwabzawa tsakanin sojojin Sudan da dakarun RSF, amma tasirin illar ƙwararan 'yan gudun hijira da sauran rikice-rikicen jinkai ya yi masa katutu.
An kwashe sama da wata biyar ana gwabza wannan yakin inda a yanzu haka, kusan kashi 80 cikin 100 na asibitocin Sudan ba sa aiki a cewar Majalisar Dinkin Duniya.
Yaɗuwar cutar zazzabin dengue
Tun kafin yaƙin Sudan, tsarin kiwon lafiyar ƙasar ke cikin mummunan yanayi da har ya gaza shawo kan ɓarkewar cututtuka da kan ɓarke a lokutan damuna na shekara-shekara da ake samu, kamar cutar zazzabin cizon sauro ta maleriya wanda ke yaduwa sosai a fadin da kasar da kuma zazzabin dengue.
A wannan shekara da Gedaref ya karbi baƙuncin sama da mutum 250,000 da ke gudun hijira a cewar Majalisar Dinkin Duniya MDD, lamarin ya ƙara yin muni.
“Gadajen asibitin duk sun cika ga shi kuma ana ƙara samun marasa lafiya, musamman yara,” a hirar da AFP ta yi da wani ma'aikacin lafiya a Asibitin Gedaref, wanda ya bukaci a sakaya sunansa.
“Adadin wadanda ke karɓar magani a gida ya zarce waɗanda ke kwance a asibiti,” in ji shi.
Amal Hussein wata mazauniyar jihar ta Gedaref ta shaida wa AFP cewa "a kowane gida, akwai akalla mutum uku da ke fama da zazzabin dengue".
Sama da yara 1,200 ne suka mutu
Zazzabin dengue cuta ce da sauro ke haifarwa, alamominta sun hada da ciwon kai da tashin zuciya da amai da ciwon gabobi, mafi muni kuma shi ne zubar jini wanda kan kai mutum ga mutuwa.
Likitoci da Majalisar Dinkin Duniya sun sha yin gargadin cewa tashe-tashen hankula a Sudan, hade da lokutan damina da rashin ababen more rayuwa za su haifar da barkewar cututtuka.
Sama da yara 1,200 ne suka mutu a sansanonin ‘yan gudun hijira tun daga watan Mayu, sakamakon barkewar cutar kyanda, a cewar hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya.
A El Fasher, babban birnin jihar Darfur ta Arewa, "an samu rahoton bullar cutar zazzabin cizon sauro kan mutum 13 a cikin mako guda", in ji ma'aikatar lafiya.
A birnin Khartoum kuwa, "mutum uku ne suka mutu sakamakon cutar Kwalara ta amai da gudawa" - a gundumar Hajj Youssef da ke gabashin babban birnin kasar, a cewar wani kwamiti da ke adawa da gwamnati kasar a ranar Litinin.
'Masifa tana ƙwanƙwasa ƙofa a Sudan'
"Ku yi taka tsantsan wajen guje wa kamuwa da cuta," in ji kwamitin - da ke zama daya daga cikin wadanda ke shirya zanga-zangar neman dimokuraɗiyya kafin aukuwar yaƙin kana waɗanda a yanzu ke ba da agaji don taimakawa mutanen da rikicin ya rutsa da su.
Matsalar rashin kiwon lafiya ta ƙara tsananta yanayin jin ƙai a Sudan, inda rabin al'ummar ƙasar miliyan 48 ke dogaro kan kayayyakin agaji don tsira da rayukansu, yayin da mutanen miliyan shida ke gab da faɗa wa cikin yunwa, a cewar MDD.
Wakiliyar Majalisar Dinkin Duniya a kasar Sudan Clementine Nkweta-Salami, ta yi wani gargadi a ranar Litinin kan cewa "Masifa tana ƙwanƙwasa ƙofa a Sudan."
Ta buƙaci ''masu ba da agaji da su gaggauta fitar da kuɗaɗen da aka alkawarta don ci gaba da bayar da agajin ceton rayuka a Sudan.''
Ya zuwa farkon watan Satumba, rikicin da ya ɓarke tsakanin babban hafsan sojin Sudan Abdel Fattah al-Burhan da tsohon mataimakinsa, kwamandan rundunar RSF Mohamed Hamdan Daglo, ya yi sanadin mutuwar kusan mutum 7,500, a cewar wani ƙiyasi da ƙungiyar masu fafutukar yaƙi da ta'addanci da tattara bayanai da wuraren da yaƙi ya auku.
Harin bama-bamai a kan asibitoci
An jefa bama-bamai a kan gomman asibitoci wasu kuma mayakan sun mamaye su, lamarin da Majalisar Dinkin Duniya ta kira da "rashin kula da fararen hula."
Ana yawan kai wa likitoci da sauran ma'aikatan jin ƙai da suka rage hari da kuma sace sauran kayayyyakin aikinsu a daidai lokacin da buƙatun mutane da ke neman taimako ke daɗa ƙaruwa.
A ranar Litinin Ma'aikatar Lafiyar kasar ta bayyana cewa dakarun RSF sun ƙwace ikon babban wurin ajiye kayayyakin kiwon lafiya.
''An yi asarar magunguna da kayayyakin aikin jinya da kudinsu ya kai dalar Amurka miliyan 500, a cewar mai magana da yawun ma'aikatar Haitham Mohammed Ibrahim.
Haitham ya yi ƙari da cewa "an yi asarar kashi 70 cikin 100 na kayayyakin da ke cibiyoyi na musamman a birnin Khartoum."
Kafin yaƙin Sudan, mutum daya cikin mutane uku a ƙasar na buƙatar tafiyar fiye da sa'a guda don samun damar kula da lafiya, kuma kashi 30 cikin 100 na muhimman magunguna da ake bukata kawai ake samu a cewar MDD.