Ƙungiyar haɓaka tattalin arzikin ƙasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) ta ce tana goyon bayan Nijeriya wajen yin watsi da zarge-zargen da ake yi mata na taimaka wa ‘yan ta’adda.
A wata sanarwar da ta fitar ranar Alhamis, ƙungiyar ta ce Nijeriya ta daɗe tana taimaka wa ƙasashen ciki da wajen Yammacin Afirka wajen tabbatar da tsaro da zaman lafiya.
“Ƙungiyar tana goyon bayan Nijeriya da sauran ƙasashen ECOWAS wajen yin watsi da zargin taimaka wa ta’addanci da aka yi musu,” in ji sanarwar.
“Nijeriya ta shafe shekaru tana tallafawa wajen zaman lafiya da samar da tsaro ba a Yammacin Afirka kaɗai ba har da nahiyar Afirka. Nasarorin baya bayan nan da rundunar haɗaka ta yaƙi da ta’addanci ta MNJTF ta samu ƙarƙashin jagorancin Nijeriya ta nuna jajircewar Nijeriya wajen samar da tsaro da zaman lafiya a yankin,” in ji ECOWAS.
Ƙungiyar ta ce saboda haka ta ce "ƙasa mai irin wannan karamci da kyautatawa ba za ta taimaka wa ta’addanci ba."
Kazalika ƙungiyar ta yi kira ga ƙasashe a yankin da su rungumi tattaunawa maimakon yaɗa "zarge-zarge da ba su da tushe."
Ranar Laraba ne dai shugaban ƙasar Nijar, Janar Abdourahmane Tiani, ya zargi jami’an gwamnatin Nijeriya da hannu wajen tallafa wa ‘yan ta’adda da ma Faransa wajen ta-da zaune-tsaye a Nijeriya da Nijar.
Tiani ya ce ƙasarsa ta sanar da jami’an leƙen asirin Nijeriya kafin a kafa ƙungiyar ta’adda ta Lakurawa a yankin Sokoto, sai dai a cewarsa, daga baya ta bayyana cewar Nijeriya tana da sani game da kafa ƙungiyar.
Bayan hirar dai, jami’a daga gwamnatin Nijeriya sun musanta zargin da Tiani ya yi suna masu cewa Nijeriya ba za ta taɓa haɗa baki da ƙasar waje domin cutar da ƙasarta ko ƙasashe maƙwabta ba.