Zambia da Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo sun amince su sake buɗe iyakoki uku da suka haɗa ƙasashen biyu a ranar Talata bayan rufe su a ƙarshen mako.
Tawagar ƙasashen biyun ƙarƙashin jagorancin ministocin kasuwancinsu ta tattauna a ranar Litinin a Kinshasa, babban birnin Kongo.
An gudanar da zaman tattaunawar ne bayan Zambia ta sanar da rufe iyakokin Kasumbalesa da Mokambo da kuma Sakania a ranar Lahadin da ta wuce, sakamakon zanga-zangar da aka yi kan hana shigo da lemon tsami da maƙwabciyarta ta yi.
"Ƙasashen biyu sun kuma amince da mutunta ƙa'idojin kasuwanci kamar yadda hukumomin yankin da kuma ƙungiyar cinikayya ta duniya suka goyi baya," in ji sanarwar da babban sakatare na harkokin kasuwanci da ciniki da masana'antu na Zambia Lillian Bwalya ya fitar bayan tattaunawar.
Izinin kwana 30
Ministan kasuwanci, ciniki da masana'antu na Zambia Chipoka Mulenga da takwaransa na Kongo Julien Paluku Kahongya ne suka sanya hannu kan sanarwar, inda Mulenga ya bayyana farin cikinsa da cewa kayayyakin Zambia za su shiga Kongo ba tare da wani takunkumi ba.
Paluku ya ce ƙasashen biyu sun kuma amince tare da ba da izinin shigar da dukkan kayayyakin da aka yi jigilarsu cikin kwanaki 30.
Zambia da Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo sun jima suna hulɗar kasuwanci a yankin, inda suke hada-hadar kayayyaki daban-daban da suka haɗa da lemon zaƙi da lemon tsami.
Aranar Litinin ne shugaban ƙungiyar masana'antun ƙasar Zambia Ashu Saga ya bayyana damuwarsa kan matakin hana shigo da kayayyakin Zambiya da Ƙongo ta ɗauka, inda ya yi kira ga ƙasashen biyu da su warware matsalolin da suka haifar da dakatarwar.