Zaben Adamawa: INEC ta bukaci 'yan sanda su tuhumi Hudu Ari

Zaben Adamawa: INEC ta bukaci 'yan sanda su tuhumi Hudu Ari

A ranar Lahadi ne INEC ta dakatar da tattara sakamakon zaben gwamna a Jihar Adamawa.
INEC din ta dakatar da tattara sakamakon zaben bayan sanarwar da Ari Yunusa ya bayar /Hoto: INEC

Hukumar zaben Nijeriya INEC ta bukaci babban sufeton ‘yan sandan kasar da ya gudanar da bincike da kuma tuhumar kwamishinan zabe na Jihar Adamawa Barista Hudu Yunusa Ari.

INEC ta sanar da hakan a shafinta na Twitter ranar Talata tana mai cewa ta cimma wannan matsaya ne bayan ta tattauna kan batun zaben gwamna a Adamawa.

Hukumar zaben Nijeriya kuma ta bukaci sakataren gwamnatin tarayya ya ja hankalin hukumar da ke da alhakin nada kwamishinonin zabe kan halin da kwamishinan zaben ya nuna domin daukar mataki.

Haka kuma INEC ta ce tattara sakamakon zaben zai ci gaba a lokacin da baturen zaben jihar ya sanar.

A ranar Lahadi ne INEC din ta dakatar da tattara sakamakon zaben gwamna a Jihar Adamawa.

Hakan ya biyo bayan ayyana Aisha Binani a matsayin gwamnan jihar Adamawa da kwamishinan zaben jihar Barista Hudu Yunusa ya yi.

Wannan lamarin ya jawo ce-ce-ku-ce da rudani ganin cewa ba huruminsa ba ne sanar da sakamakon zaben.

Hakan kuma ya sa INEC din ta yi gaggawar fitar da sanarwa ta yi watsi da sakamakon da Hudu ya sanar tare da nuna cewa ya kwace aikin baturen zaben jihar.

Bayan haka kuma INEC din ta dakatar da shi daga aikinsa.

An gudanar da zabe a zagaye na biyu a Jihar Adamawa tsakanin gwamna mai ci a Ahmadu Fintiri na Jam’iyyar PDP da kuma Sanata Aishatu Binani ta Jam’iyyar APC.

TRT Afrika da abokan hulda