Dubban daruruwan mazauna da kuma mutanen da suka rasa matsugunansu a halin yanzu suna cikin barazanar kamuwa da yunwa, a cewar MDD. / Hoto: Reuters

Rundunar RSF ta Sudan ta sanar da cewa za ta bayar da dama ga masu neman ficewa daga birnin El-Fasher na Darfur wanda ke fama da yaƙe-yaƙe tsawon makonni.

Rundunar ta RSF wadda ke yaƙi da sojojin ƙasar fiye da shekara ɗaya ta bayyana haka ne a wata sanarwa da ta fitar a ranar Juma’a da dare inda ta ce ta shirya taimaka wa ƴan ƙasar ficewa zuwa wasu wuraren domin neman mafaka.

El-Fasher, wanda shi ne babban birnin Arewacin Darfur, ya taɓa kasancewa ɗaya daga cikin wuraren da ke karɓar ƴan gudun hijira inda da dama daga cikinsu ke taruwa domin samun mafaka.

Dubban daruruwan mazauna da kuma mutanen da suka rasa matsugunansu a halin yanzu suna cikin barazanar kamuwa da yunwa, a cewar MDD.

Abokan juna sun zama na gaba

Dakarun na RSF sun yi kira ga mazauna El-Fasher da “su guji wuraren da ake fama da rikici da kuma wuraren da sojojin sama za su iya kai wa hari, kada su amsa munanan kiraye-kirayen da ake yi na tara jama’a da jawo su cikin yaƙi”.

Kasar Sudan dai ta shafe sama da shekara guda tana fama da rikici tsakanin sojojin ƙasar karkashin jagorancin shugaba Abdel Fattah al-Burhan da kuma RSF karkashin jagorancin tsohon mataimakinsa Mohamed Hamdan Daglo.

Rikicin ya yi sanadiyar mutuwar mutane kusan 15,000 a El-Geneina babban birnin jihar Darfur kadai, a cewar kwararrun Majalisar Dinkin Duniya.

Kungiyar agajin likitoci ta Doctors Without Borders a ranar Laraba ta ce asibitinta da ke arewacin Darfur ya karbi fiye da mutum 450 da aka kashe a fadan da aka gwabza tun ranar 10 ga watan Mayu, amma ta yi nuni da cewa, adadin wadanda suka mutu ya zarce haka.

AFP