Mumunan yakin  ya haifar da daya daga cikin mafi munin matsalar jinƙai a duniya/Hoto: AFP

Amurka wadda ke shiga tsakani za ta fara zaman tattaunawa a ƙasar Swizerland a ranar Laraba kan yaƙin Sudan da tsagaita wuta, duk da shirin gwamnatin ƙasar na ƙauracewa taron.

Tom Perrielo, jakadan Amurka na musamman a Sudan, wanda ya kira taron tattaunawar, ya ce za su ci gaba da taron duk kuwa da rashin halartar gwamnatin Sojin Sudan, yana mai cewa al'ummar Sudan da yaƙi ya jefa cikin mummunan yanayi ba za su iya jira ba.

Tun a watan Afrilun 2023 ne yaƙi ya barke tsakanin sojojin Sudan (SAF) ƙarƙashin jagorancin shugaban sojojin ƙasar Abdel Fattah al Burhan da kuma dakarun gaggawa ta (RSF), karkashin jagorancin tsohon mataimakinsa Mohamed Hamdan Daglo.

Sai dai, a yayin da tawagar RSF ta isa Switzerland domin halartar taron tattaunawar wanda zai gudana ta bayan fage a wani wuri da ba a bayyana ba, har yanzu dakarun sojin Sudan (SAF) ba su amince da goron gayyatar ba.

Za a shafe tsawon kwanaki 10 ana gudanar da taron tattaunawar wanda ƙasar Saudiyya da Switzerland suka ɗauki nauyi, inda ƙungiyar Tarayyar Afirka (AU) da Masar da Hadaddiyar Daular Larabawa da kuma Majalisar Dinkin Duniya duk za su kasance a wurin.

Mummunan yaƙin ya haifar da ɗaya daga cikin mafi munin matsalar jinƙai a duniya.

Yaƙin ya yi sanadiyar tilastawa mutum ɗaya cikin mutane biyar barin matsugunansu, yayin da dubbai suka mutu.

Fiye da mutane miliyan 25 a faɗin Sudan waɗanda ke wakiltar rabin al'ummar ƙasar suna fama da tsananin yunwa.

''Yanzu ne lokacin samun zaman lafiya'' in ji Perrielo a ranar Talata.

"Ya zuwa yanzu, Rundunar Sojin Sudan ba ta ba da amincewarta ga goron gayyatar da aka aika mata ba. Amma duk da haka za mu ci gaba da zaman tare da abokan hulɗar mu na kasa da kasa da na fasaha don gano duk wata hanya da za a bi wajen tallafawa al'ummar Sudan,'' in ji shi, yana mai ƙira ga gwamnatin da ta "yi amfani da wannan damar".

'Bukatar gaggawa'

Tattaunawar baya da aka gudanar a birnin Jeddah na Saudiyya ba ta haifar da ɗa mai ido ba.

Idan har ya zuwa yanzu kujerun SAF suka kasance babu kowa, ba za a iya yin sulhu tsakanin bangarorin da ke yaki da juna ba, sai dai sauran waɗanda suka samu halartar taron su ci gaba da aiwatar da ajandar tattaunawar.

"Al'ummar Sudan ba za su iya juriyar, har sai mun jira ba.''

Wani mamba na tawagar RSF ya tabbatar da cewa suna Switzerland gabannin taron tattaunawar.

"Tawagarmu ta isa Geneva domin fara taron tattaunawar; ba mu san komai game da tawagar sojojin Sudan ba," Kamar yadda mamban ya shaida wa AFP a ranar Talata.

Gwamnatin Sudan ta ce ana buƙatar ƙarin tattaunawa kafin a shiga yarjejeniyar tsagaita buɗe wuta.

Ministan yada labarai na Sudan Graham Abdelkader ya ce ƙasar ba za ta amince da ''duk wani sabbin masu sa ido ko mai shiga tsakani ba'' bayan da Washington ''ya nace kan shigar da Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE)cikin batun a matsayin mai sa ido.''

Sojojin Sudan dai sun sha zargin UAE da goyon bayan RSF.

AFP