Za a soma shari'ar manyan shugabannin kamfanin mai kan zargin laifukan yaki a Sudan

Za a soma shari'ar manyan shugabannin kamfanin mai kan zargin laifukan yaki a Sudan

Ana zargin shugabannin da hannu a kisan kiyashi da aka yi a wani kauye wanda ke makwabtaka da wurin da ake hakar fetur.
Ana ganin wannan shari'ar za ta kasance mafi girma a tarihin Sweden, bayan shafe shekara 13 ana bincike, Hoto/ Getty Images

Tsofaffin shugabanni biyu a wani kamfanin mai na kasar Sweden za su gurfana a gaban wata kotu da ke Stockholm a ranar Talata inda ake zarginsu da hannu a aikata laifukan yaki da gwamnatin Sudan ta yi daga 1999 zuwa 2003.

Ana zargin Swede Ian Lundin da Alex Schneiter da neman gwamnatin Sudan ta ba su sojoji domin kula da daya daga cikin wuraren hakar mai na Lundin, wanda daga baya aka kai wa hari ta sama da kashe farar-hula da kona kauye baki daya, kamar yadda mai shigar da kara ya bayyana.

Lundin shi ne shugaban kamfanin mai na Lundin Oil, wanda a halin yanzu ya koma Orron Energy, daga 1998 zuwa 2002, kuma Schneiter shi ne mataimakin shugaban kamfanin a lokacin.

Sai dai duka mutum biyun sun musanta zarge-zargen.

Mafi grima a tarihi

Ana ganin wannan shari’ar ita ce za ta kasance mafi girma a tarihin Sweden, bayan shafe shekara 13 ana bincike, inda aka rubuta rahoto mai shafi 80,000.

Mutanen biyu da a baya aka bayyana su a matsayin wadanda ake zargi a 2016, suna fuskantar tuhuma kan “hannu a manyan laifukan yaki” wadanda aka aikata a zamanin mulkin Omar al-Bashir.

Bayan kamfanin Lundin ya hako mai a 1999 a rijiyar “Block 5A” wadda a yanzu take a Sudan ta Kudu, sojojin Sudan tare da wasu masu dauke da makamai wadanda suke kawance da su, “sun kaddamar da farmaki domin kwace iko da yankin da kuma saka sharudda da suka dace don hakar mai na kamfanin Lundin,” kamar yadda hukumar da ke shigar da kara ta Sweden ta sanar a lokacin da take karanto tuhume-tuhumen.

Labari mai alaka: Fafutukar neman mulkin da ta rikide zuwa mummunan yaki a Sudan

“A namu ra'ayin, binciken ya nuna cewa sojoji da dakarun sa-kai sun kai hari kan fararen-hula tare ko kuma sun kai hare-haren kan mai uwa da wabi," in ji mai shigar da kara na gwamnati Henrik Attorps.

Hare-hare kan farar-hula

Wannan ya hada da “hare-hare daga jiragen sama, harbin farar-hula daga jirage masu saukar ungulu, garkuwa da mutane da kuma sace kayayyakin farar-hula da kone kauyuka baki daya.”

Masu shigar da kara sun ce wadanda ake zargin suna da hannu kan lamarin saboda kamfanin Lundin na sane da cewa bukatar gwamnatin Sudan ta ba ta sojoji domin tsaronta na nufin za ta kwace iko da yankin da “karfin soji”.

“Abin da ya sa suke da hannu a laifin shi ne sun bukaci hakan duk da sun fahimci cewa sojoji da kuma ‘yan sa-kai su yi irin wannan yakin ya saba wa dokar kasa da kasa kan hakkin bil adama,” kamar yadda babban mai shigar da kara Krister Petersson ya bayyana.

Idan aka kama su da laifi, Lundin da Schneiter za su iya fuskantar daurin rai da rai. Tuni masu shigar da kara suka bukaci a haramta wa mutum biyu yin wata yarjejeniya ta kasuwanci ta tsawon shekara 10.

‘Bata lokaci’

Masu shigar da karar sun kuma bukaci a kwace kimanin dala miliyan 218 daga kamfanin Orron Energy, wanda ya zo daidai da ribar da kamfanin ya samu bayan sayar da aikinsa na Sudan a 2003.

Sai dai masu kare wadanda ake zargin sun bayyana cewa wannan shari’ar na jawo jinkiri.

“Ra’ayinmu shi ne wadannan shekaru biyun wadanda za a yi a kotun gunduma babban bata lokaci ne da kuma dukiya,” kamar yadda Torgny Wetterberg ya bayyana a jajibirin shari’ar, wanda shi ne lauyan Ian Lundin.

Wetterberg ya ce masu tsaron ba su yarda da bayanin da masu gabatar da kara suka yi ba game da abubuwan da suka faru, kuma sun gina shari'arta kan da'awar yanayi ba tare da wata kwakkwarar hujja ba.

Wetterberg ya bayyana cewa ba su amince da bayanin da masu shigar da kara suka gabatar kan abubuwan da suka faru inda ya yi zargin cewa sun shigar da kara ba tare da wata kwakkwarar hujja ba.

“Daga yadda muke kallon lamarin, abin mamaki ne yadda mai shigar da karar ya ci gaba da wannan shari’ar,” Wetterberg ya bayyana cewa yana da tabbaci kan cewa masu shigar da karar ba za su samu abin da suke so ba na kama wadanda suka shigar kara da laifi.

Laifuka a kasashen waje

Sweden za ta iya hukunta laifuka wadanda aka yi a kasashen waje a kotunanta, duk da cewa dole gwamnati ta amince kafin a tuhumi wani dan kasar waje kan laifukan da aka aikata a waje.

A lokacin da aka gabatar da tuhumar, Schneiter ya kalubalanci shari’ar inda ya bayyana cewa shi ba dan kasa bane ko mazaunin kasar wanda a cewarsa ba za a iya tuhumarsa ba.

Sai dai Kotun Kolin Sweden ta yi watsi da batunsa inda ta yanke hukunci a Nuwambar 2022 kan cewa “akwai bukatar wata alaka da Sweden” domin tuhumarsa, kuma dangantakar da ke tsakaninsa da Schneiter kawai “ta isa”.

AFP