Kakakin Majalisar Dokokin Ghana Mista Alban Sumana Kingsford Bagbin ya gargadi ‘yan majalisar kasar da ke zuwa a makare da su guji wannan dabi’ar inda ya tabbatar da cewa za a soma rufe kofar majalisar daga 10:00 na safe a duk ranar da ake zama.
Kamfanin dillancin labarai na Ghana ya ruwaito kakakin majalisar yana cewa ya dauki matakin ne sakamakon yadda mambobin majalisar ke halartar zaman majalisar.
“Masu girma ‘yan majalisa, za a rinka kulle wadanda suka makara a waje har zuwa lokacin da kakakin majalisa ya bayar da umarnin sake bude kofar.
Za a rinka rufe kofar da misalin goma na safe. Kakakin Majalisa zai kasance a ciki kuma za a dauki lokaci kafin a bude kofar,” in ji Kakakin Majalisar.
“Idan ba za ku iya bin haka ba, mu amince kan cewa za mu rinka zaman majalisar da rana, daga karfe biyu ko kuma hudu. Kwamitoci za su rinka tattaunawa da safe; sai su rinka bayar da rahoton da za mu duba da rana; zuwa lokacin sai mu tashi da misalin takwas na safe idan cunkoson ababen hawa ya ragu,” in ji shi.
Ya bayyana cewa idan mambobin majalisar sun gaza cimma matsaya za a soma aiwatar da shawarar da aka bayar game da lamarin a zaman majalisar na gaba.
Kakakin Majalisar ya kuma bayar da shawara kan majalisar ta yi zama na musamman a ranar Asabar, 16 ga watan Disamba domin rage dumbin ayyukan da suke kanta.