Hukumar Kula da 'Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya, UNHCR, ta ce a halin yanzu akwai 'yan hijira miliya 6.2 a kasar Kongo. / Hoto: AP

'Yan gudun hijira akalla 60 ne suka mutu sakamakon matsananciyar yunwa a lardin Kwilu da ke tsakiyar kasar Kongo, a cewar Hukumar Jinkai ta yankin a ranar Juma'a.

Gidan rediyon Majalisar Dinkin Duniya da ke Kongo ya ce an raba fiye da mutum 4,600 da muhallansu a garin Kwamouth da ke yankin Mai-Ndombe kuma yanzu haka suna zaune ba tare da abinci da sauran kayayyakin rayuwa ba bayan sun tsere zuwa garin Bandundu da ke lardin Kwilu.

Babban jami'i a Hukumar Jinkai ta Kwilu, Frederic Nkumpum, ya ce mutanen sun mutu ne tun daga lokacin da suka isa garin Bandundu a karshen watan Agusta.

“Gaba daya, yara 33 da manya 27 ne suka mutu. A cikin manyan, mata 17 ne yayin da maza 10 ne suka mutu. Akwai matsaloli na rayuwa da suka kunno kai domin kuwa wadannan mutanen ba su samu wani taimako ba, ko da na abinci ne,” a cewarsa.

Nkumpum ya ce Hukumar Jinkai ta Lardin tana neman agaji domin bai wa mutanen da ke cikin wannan mummunan yanayi.

“A nan Bandundu, 'yan gudun hijirar sun kai 4,669. Suna matukar bukatar taimako. Muna ci gaba da mika kokon bararmu domin a taimaka musu don suna shan wahala,” in ji shi.

Matsalar 'yan gudun hijira ta zama ruwan-dare a Kongo inda 'yan tawaye da masu rike da makamai kan kai hare-hare a kauyuka suna kashe mutane, abin da ke sa wa wasu su tsere daga muhallansu.

Hukumar Kula da 'Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya, UNHCR, ta ce a halin yanzu akwai 'yan hijira miliyan 6.2 a kasar Kongo.

AA