Daga Mazhun Idris
Ana ganin kamar an kama hanyar mantawa da yakin Sudan duk da cewa akwai yara miliyan 14 da ke bukatar agaji, kamar yadda Asusun Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ya yi gargadi.
"Akwai akalla yaran Sudan miliyan 14 da suke bukatar taimako. Hakan yana nufin daya cikin kowane yara biyu da ke Sudan," a cewar Ted Chaiban, Mataimakin Darakta a UNICEF kan Ayyukan JinKai a Sudan.
Rikicin wanda yake cikin wata na hudu da farawa "ya shafi yara ta hanyoyin da ba a taba gani ba," in ji Chaiban bayan da ya kai ziyara inda yakin ya shafa.
Ya kara da cewa: "Wannan mummunan rikici ne wanda dole mu yi dukkan mai yiwuwa mu taimaka wa yara da iyalansu yayin wannan lokaci na bukata."
Matsalar halin jinkai
Sudan ta fada cikin mummunan yaki fiye da wata uku kenan, bayan fara fada a watan Afrilu tsakanin dakarun Sudanese Armed Forces (SAF) da na Rapid Support Forces (RSF).
Rikicin ya yi sanadin mutuwar daruruwan mutane da jikkata dubbai, inda aka tilasta wa 'yan Sudan da dama fadawa matsanancin bukatar taimakon agaji, wanda ba a taba ganin irinsa a baya ba.
Tafiya ta kai mataimakin daraktan UNICEF zuwa Sudan da makwabciyarta Chadi a cikin wata tawaga yare da Mataimakiyar Shugabar Majalisar Dinkin Duniya, inda suka gana da iyalai da ke kan iyaka wadanda suka fito daga Sudan bayan sun tsere wa yakin.
"Na zo ne saboda wani babban aiki na jan hankali kan halin da ake ciki a Sudan da makwabciyarta," in ji Chaiban.
Samar da hanyar kai taimakon jinkai
Yakin Sudan ya jawo matsanancin karancin abinci da ruwa da magunguna da man fetur yayin da farashin muhimman abubuwa suka yi tashin gwauran zabo.
UNICEF ya yi kira ga bangarorin biyu da su bayar da dama a aika da kayan agaji a wuraren da ake yakin.
"Akwai abokan aikinmu da dama aka kashe tun farkon fara yakin kuma hakan abin takaici ne. Game da UNICEF, ma'aikatan biyu ne suka rasa 'ya'yansu sanadin yakin kuma wasu ma'aikatan agaji na MSF da aka doka a Khartoum," in ji shi.