Uganda ta kashe masu tayar da kayar baya 560 da ke da alaka da mayakan IS tun bayan kaddamar da farmaki a kansu a watan Disamban 2021, a cewar Shugaban kasar Yoweri Museveni.
Kungiyar kawance da ke yaki da Kampala ta Allied Democratic Forces (ADF) ta kafa sansaninta a cikin dazuzzukan da ke yankin gabashin Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo, inda take kai hare-hare a kasashen Kongo da Uganda.
Bayan samun izini daga Kongo, sojojin Uganda sun kaddamar da farmaki kan kungiyar ADF a dazukan, inda suka yi nasarar lalata sansanonin mayakan da kuma kama da dama daga cikinsu.
A wani jawabi da ya yi a yammacin ranar Alhamis, Shugaban Uganda Museveni ya ce hare-haren sojin kasar sun yi sanadin kashe mayakan kungiyar ADF 567 tare da kama mutum 50 daga cikinsu.
Kazalika ya bayyana cewa, an kwato wasu manyan bindigogi da makaman roka 167 daga hannun ‘yan tawayen.
"Sun wahala sosai... ba su da wani zabi da ya rage musu illa mika wuya," in ji Museveni.
Museveni ya yi kira ga masu tuka motocin bas- bas da ‘yan kasuwa da otal-otal a Uganda da su yi taka tsantsan, tare da sa ido da kuma daukar duk wasu bayanai na abokan cinikinsu don dakile hanyoyin da 'yan kungiyar ADF za su iya bi ko amfani da kayayyakinsu wajen kai hare-hare.
A makon nan ne, 'yan sandan Uganda suka ce sun kwato bama-bamai akalla shida da maharan ADF suka shirya amfani da su, ciki har da wanda suka samu daga wani dan kunar bakin-wake da ke shirin shiga wani coci.
A wasu hare-hare biyu mafi muni da kungiyar ta kai Uganda, akwai wani harin kunar bakin wake da aka kai a shekarar 2021 a wajen wani babban ofishin 'yan sanda a babban birnin kasar, da kuma kusa da ginin Majalisar Dokoki, wanda ya yi sanadin mutuwar mutum bakwai.
A watan Yunin shekarar nan, an kashe mutum 42 wadanda akasarinsu dalibai ne daga wata makaranta da ke yakin Kasese a yammacin Uganda.