Rahotanni sun ce gwamnan soji na lardin Kivu ta Arewa na Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kongo ya rasu sakamakon raunukan da ya samu bayan harbinsa da bindiga da aka yi a fagen daga a wani farmaki da 'yan tawayen M23 suka kai.
'Yan tawayen na ci gaba da tunkarar babban birnin lardin wato Goma ta bangarori biyu, inda ake fama da tashin hankali inda dubban jama’a ke ci gaba da tserewa kuma Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa tashin hankalin na iya rikidewa zuwa babban yakin yanki.
Manjo Janar Peter Cirimwami Nkuba, wanda ya jagoranci lardin tun a shekarar 2023, ya rasu a ranar Alhamis, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters da AP suka ruwaito, suna ambato rahoton Majalisar Dinkin Duniya da jami'an gwamnati.
Rahoton na cikin gida na Majalisar Dinkin Duniya da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya gani ya ce ya samu rauni ne a lokacin da yake duba sojoji a wani wuri mai tazarar kilomita 20 (mil 12) daga Goma.
Rahoton ya kara da cewa, "An ruwaito cewa daga baya ya mutu da safiyar Alhamis yayin da aka dauke shi da jirgin sama daga Goma domin ci gaba da jinya."
Fadan dai ya fi kamari a gabashin Kongo mai arzikin ma'adinai tun farkon wannan shekara yayin da kungiyar M23 ta kwace iko da wasu yankuna fiye da kowane lokaci.