‘Yan sandan Nijeriya sun ba da matakan kare kai daga kutsen intanet

‘Yan sandan Nijeriya sun ba da matakan kare kai daga kutsen intanet

Jama'a da dama a Nijeriya na fadawa hannun 'yan damfara inda ake tafka asarar kudade masu dumbin yawa.
'Yan sandan sun yi gargadi kan a guji amfani da abubuwan da za a yi saurin hasashe kamar ranar haihuwa ko kuma sunaye. Hoto/TRT Afrika

‘Yan sandan Nijeriya sun fitar da hanyoyin da za a kare kai daga kutsen.

A wani sako da ‘yan sandan suka wallafa a shafinsu na intanet, sun bayar da wasu shawarwari wadanda suka ce za su taimaka matuka ga masu amfani da intanet.

Ga wasu daga cikin shawarwarin:

Amfani da lambobi ko kalmomi na sirri masu karfi:

‘Yan sandan sun bayar da shawarar akwai bukatar a rinka saka lambobin sirri ko kuma password masu karfi wadanda suka hada da manyan bakake da kanana da lambobi da alamomi.

Sun yi gargadi kan a guji amfani da abubuwan da za a yi saurin hasashe kamar ranar haihuwa ko kuma sunaye.

Haka kuma ‘yan sandan sun bukaci masu amfani da wayoyi kan su rinka saka tsarin Two-Factor Authentication (2FA) wanda tsari ne da ke bayar da damar kara tsaurara tsaro a na’urori ta hanyar bukatar tantancewa har iri biyu kafin mutum ya shiga wani shafi nasa.

Bayan haka kuma ‘yan sandan sun yi gargadi kan a daina biye wa masu kokarin jawo hankali ta hanyar turo sakon email ko sms ko kuma amfani da wasu dabaru domin bayar da wasu bayanai a kanku.

Sun bayar da shawara kan tantance bayanai kan wanda ya turo sako kafin shiga sakon.

A cikin shawarwarin da suka bayar, sun kuma bukaci masu amfani da wayoyi ko kwamfuta kan su rinka sabunta manhajoji.

Sabunta manhajojin kan kunshi karin kariya daga masu kokarin kutse.

Domin kare kai daga masu kutse, ‘yan sandan sun bayar da shawara kan a rinka sayayyar kayayyaki daga shafukan da aka sani sosai.

Wani abu da ake yawan tura wa mutane ta waya shi ne sakon garabasa ko kuma kyaututtuka. ‘Yan sandan sun ja hankali kan a kiyayi irin wadannan sakonnin.

Haka kuma ‘yan sandan sun bayar da shawara kan kiyaye rarraba bayanai game da kai da suka hada da lambar banki ta BVN da lambar asusun ajiya na banki da lambobin sirri.

TRT Afrika