‘Yan sanda a Birtaniya sun ce sun tuhumi tsohuwar Ministar Man Fetur ta Nijeriya Diezani Alison-Madueke da zargin cin-hanci.
A ranar Talata, ‘yan sandan sun bayyana cewa suna zargin Diezani da karbar cin hanci domin bayar da kwangilolin man fetur da gas na miliyoyin famafamai.
Alison-Madueke mai shekara 63, na daga cikin manyan kusoshin gwamnatin Tsohon Shugaban Nijeriya Goodluck Jonathan inda ta yi ministar man fetur daga 2010 zuwa 2015.
Haka kuma ta yi shugabar riko ta kungiyar kasashe masu arzikin man fetur ta OPEC.
“Muna zargin Diezani Alison-Madueke da amfani da karfinta a Nijeriya inda ta karbi cin-hanci domin bayar da kwanigilolin miliyoyin famafamai,” in ji Andy Kelly, shugaban Hukumar da ke Yaki da Laifuka ta Amurka NCA.
Shugaban NCA ya bayyana cewa ana zargin Alison-Madueke da samun akalla fam dubu dari lakadan da amfana ta hanyar hawa jiragen sama masu zaman kansu da samun damar zuwa hutu irin na alfarma da iyalanta da kuma amfani da kadarori da dama a birnin Landan.