Shugaba Tinubu ya ce Nijeriya na fuskantar manyan kalubale da ke bukatar jami'an gwamnati su kasance masu gaskiya da sanin makamar aiki./Hoto: Fadar Shugaban Nijeriya

'Yan Nijeriya sun bayyana korafe-korafensu game da yawan ministocin da shugaban kasar Bola Ahmed Tinubu ya rantsar domin yin aiki a gwamnatinsa.

An rantsar da ministoci 45 ranar Litinin a Abuja, kasa da mako guda bayan shugaban kasar ya sanar da ma'aikatun da za su jagoranta.

Sai dai wasu sun soki shugaban kasar a kan yawan mutanen da ya nada a mukaman ministocin yayin da kasar ke fama da matsalolin tabarbarewar tattalin arziki, suna masu cewa ana kashe biliyoyin kudi kan ministoci da 'yan tawagarsu yayin da talaka ke dandanda kudarsa.

"Ministocin sun yi yawa sosai idan aka kwatanta da na gwamnatocin baya. Hakan zai sa kasar ta rika kashe kudi sosai a kan biyan albashi da dawainiyar ministocin 45 da masu taimaka musu da motocin da suke hawa da sauransu a yayin da tattalin arzikin Nijeriya ke cikin mawuyacin hali, sannan kasar na cikin kangin bashi," a cewar Musa Njadvara, wani masanin tattalin arziki, a hirarsa da kamfanin dillancin labaran Anadolu na kasar Turkiyya.

Ya kara da cewa a halin da ake ciki Nijeriya na kashe kashi uku cikin hudu na kasafin kudinta wajen gudanar da gwamnati da biyan albashi da alawus-alawus.

Chukwudi Odoeme, wani farfesa kan aikin lauya a Abuja, ya ce kundin tsarin mulkin kasar ya wajabta nada minista daya daga kowace jiha cikin jihohin kasar 36 da babban birnin tarayya.

Ya kara da cewa bai kamata ministocin su kai 45 idan da a ce shugaban kasar ya yi biyayya ga kundin tsarin mulkin Nijeriya.

"Majalisar ministocin ta yi yawa sosai kuma ba ta da ma'ana," kamar yadda ya shaida wa Anadolu.

Ya ce shugaban kasar ya saka wa mutanen da suka taimaka masa wurin cin zaben da aka gudanar ranar 25 ga watan Fabrairun ne kawai.

A lokacin da yake jawabi yayin rantsar da ministocin, Shugaba Tinubu ya amince cewa Nijeriya na fuskantar manyan kalubale da ke bukatar jami'an gwamnati su kasance masu gaskiya da sanin makamar aiki.

"Kalubalen da muke fuskanta a yau yana da yawa. Muna da damar aiwatar da sauye-sauyen da aka dade ba a yi ba wadanda za su kawo zaman lafiya da ci-gaban al'ummarmu. Dole mu yi aiki domin cika muradun mutanenmu," in ji shi.

AA