Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya yaba wa kamfanin makamashi na NIPCO bisa sanya hanayen-jari a kan harkokin tsukakkiyar iskar gas wato Compressed Natural Gas (CNG) yana mai cewa hakan zai bunƙasa harkokin kasuwancin ƙasar.
Ya yaba wa kamfanin ne ranar Talata a lokacin da shugabanninsa suka kai masa ziyara a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, kamar yadda kakakin shugaban ƙasa Bayo Onanuga ya bayyana a sanarwar da ya fitar .
Shugaba Tinubu ya ce rawar da NIPCO yake takawa a harkokin makamashin Nijeriya tana da matuƙar muhimmanci wajen tabbatar da ganin 'yan ƙasar sun rungumi CNG a matsayin muhimmin zaɓi kuma mai rahusa idan aka kwatanta da fetur.
“Masu amfani da ababen hawa a Nijeriya suna da zaɓin sayen lita ɗaya ta fetur a kan N1,000 ko kuma kwatankwacinta wato kyubik mita ɗaya ta gas a kan N200. Kazalika mun sauƙaƙa wa masu ababen hawa na haya ta yadda za su iya sauya ababen hawansu daga masu amfani da fetur zuwa masu amfani da gas a kyauta,” in ji Shugaba Tinubu.
Shugaban Nijeriya ya ce amfani da CNG yana da matuƙar muhimmanci saboda ba ya gurɓata muhalli kuma yana da araha.
A nasa ɓangaren, shugaban kamfanin NIPCO, Mr Ramesh Kasangra, wanda ya jagoranci tawagar jami'an kamfanin, ya jinjina wa Shugaba Tinubu bisa jajircewarsa wajen goyon bayan fannin makamashi na CNG.
Ya ce kamfanin NIPCO zai kyautata alaƙa da gwamnatin Nijeriya domin tabbatar da ɗorewar ƙudurinta na samar da makamashi mai araha da tsafta.