Zababben shugaban Nijeriya mai jiran gado Bola Ahmed Tinubu ya bayyana wasu sakonnin fatan alheri ga Shugaba Muhammadu Buhari mai barin gado.
Tinubu ya yi kalaman fatan alherin ne a wajen bikin ba shi lambar girma mafi daraja ta Nijeriya, GCFR.da Shugaba Buhari ya yi ranar Alhamis a Abuja, babban birnin kasar.
Kazalika shugaban kasar mai barin gado ya bai wa mataimakin shugaban kasar mai jiran gado, Kashim Shettima lambar girmamawar ta biyu a daraja wato GCON.
Ga jerin kalamai 19 da Bola Ahmed Tinubu ya yi kan Shugaba Buhari:
1. Na gode Mai Girma Shugaban Kasa da ba mu wannan lambar girma mafi daraja ta kasa da ka yi ni da mataimakina Shettima.
2. Muna kuma mika godiyarmu sosai kan kammala takardu da bayanan mika mulki da irin aiki tukuru da kwamitin mika mulkin ya yi, karkashin Sakataren Gwamnatin Tarayya.
3. Takardun sun yi takaitaccen bayani kan dumbin ayyukan da gwamnatinka ta yi. Ayyuka ne masu ban sha’awa da suka cancanci yabo.
4. Ka kafa tarihi kuma babu wanda zai iya kawar da gudunmawar da ka bayar wajen ci-gaban kasarmu.
5. Sadaukarwarka wajen ci-gaba da wanzar da gwamnatin dimokuradiyya da shugabanci nagari ba za su misaltu ba.
6. A don haka ne, nake tsaye a nan wajen cike da karsashi da kyakkyawan fata da sadaukarwa ga inganta kasarmu.
7. Ina kuma cike da alfahari, amma wannan alfahari da nake ji ba a kaina ba ne. Alfahari ne na abin da wannan lokaci yake nunawa.
8. Wannan biki na yau hujja ce da ke nuna cewa Nijeriya tana kan turbar dimokuradiyya mai karfi. Dukkanmu a nan mun shaida wannan kyakkyawan koyi inda shugaba ke bai wa magajinsa lambar girmamawa.
Sannan wannan shugaba ya yi matukar kokarinsa wajen mika dukkan al’amuran gwamnati don tabbatar da shirya mai jiran gadonsa tsaf wajen karbar aikin da ke gabansa.
9. Wannan zauren ya kaure da girmama dimokuradiyyarmu da yakinin cewa wannan girmamawa za ta ci gaba da wanzuwa tsawon lokaci mai zuwa.
10. Al’amarin yau ya fi gaban a kira shi biki kawai. Yana tabbatar da cewa hanyarmu mai bullewa ce kuma babu abin da zai dakatar da mu daga bin ta.
11. Ba ko yaushe ne abubuwa za su zo mana cikin sauki ba. Amma duk da haka muna cike da karsashi da yakini kan cewa hada hannunmu waje guda zai sa mu iya shawo kan matsalolin da muke fuskanta.
12. Shugaba Buhari, ka nuna karfin hali wajen daukar tsauraran matakan da wasu suka guji dauka.
13. Daya daga cikin irin wadannan matakai su ne na bayyana gaskiyar rashin adalcin da aka yi na rushe zaben shekarar 1993, ta hanyar ayyana ranar 12 ga watan Yuni a matsayin Ranar Dimokuradiyya ta Kasar, tare da bai wa marigayi MKO Abiola lambar girma mafi daraja ta kasa.
14. Ka yi kurewar abin da duk wani mutum zai iya, ta hanyar komawa baya a waiwayi tarihi wajen yin abu mai muhimmanci da ya wanke zukata da dama masu cike da fushi.
15. Wannan adalci da ka yi kan wannan batu ya yi matukar tasiri ga halin da ake ciki a yau.
16. Ni mutum ne mai saukin hali da ya ci gajiyar goyon baya da fatan alherin al’ummar Nijeriya.
17. Mutane sun amince da mu. Ka yi naka kokarin, Mai Girma Shugaban Kasa.
18. A yanzu da babban nauyi ya hau kaina, na fahimci ma’anar wannan lambar girma da aka ba ni a yau da kuma babban aikin da ke gabana.
19. Dole na yi wannan aiki kuma dole na yi shi da kyau. Dole mu yi kokarinmu a fannin tsaro da tattalin arziki da harkar noma da ayyuka da ilimi da lafiya da wutar lantarki da dukkan bangarori.
Mutane sun cancanci a yi musu hakan. A kan wannan tafarki, ba zan ba su kunya ba kuma kai ma ba zan ba ka kunya ba, Ya Mai Girma Shugaban Kasa.