'Yan bindiga sun kai sabbin hare-hare a ƙauyuka uku na Jihar Zamfara da ke arewacin Nijeriya ranar Juma'a da daddare inda suka yi awon gaba da mutum fiye da 100, kamar yadda dagatai da mazauna yankunan suka tabbatar.
Dagacin ƙaramar hukumar Birnin-Magaji da ke Jihar ta Zamfara, Alhaji Bala, ranar Asabar ya tattabar da aukuwar lamarin, inda ya ƙara da cewa maharan sun yi dirar mikiya a ƙauyukan Gora, Madomawa da Jambuzu kuma waɗanda aka yi garkuwa da su sun haɗa da maza 38 da mata 67 da ƙananan yara da dama.
Ya ƙara da cewa, "Amma mutanen da aka sace suna iya fin haka yawa".
Shi ma Aminu Aliyu Asha, dagacin ƙauyen Madomawa, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa gomman 'yan bindiga a kan babura ne suka kai musu hari inda suka yi ta harbe-harbe sannan suka sace mutane da dama.
"Wannan garkuwa da mutane da 'yan bindiga suka yi ta keta yarjejeniyar zaman lafiya da muka ƙulla da su. A watan Fabrairun da ya wuce, mun ba su maƙudan kuɗaɗe domin kada su kawo mana hari," in ji shi.
Yunƙurin jin ta bakin kakakin rundunar 'yan sandan jihar Zamfara Yezid Abubakar, ya ci tura.
Sai dai Nusa Sani, wani mazaunin ƙauyen Madomawa, ya ce 'yan'uwansa biyu na cikin waɗanda aka sace.
Kazalika shi ma Garba Kira ya ce cikin waɗanda 'yan bindigar suka yi garkuwa da su har da fasinjoji 15 na wata motar haya da ke kan hanyar zuwa ɗaya daga cikin ƙauyukan.
Jihar Zamfara ta daɗe tana fama da matsalar masu garkuwa da mutane domin karɓar kudin fansa waɗanda ke sace mutane a cikin gaguruwansu da ɗalibai da sauransu.
A watan jiya, Babban Mai Bai wa Shugaban Nijeriya Shawara kan Sha'anin Tsaro, Malam Nuhu Ribadu ya ce akwai jagororin ’yan bindiga kimanin 300 a yankuna daban-daban da ke arewacin ƙasar, lamarin da ya sake fitowa da girman matsalar tsaro, musamman a arewacin Nijeriya