Hukumomi a Nijeriya sun ce 'yan bindiga sun yi garkuwa da ɗaliban kiwon lafiya aƙalla 20 a jihar Benue da ke tsakiyar ƙasar.
An sace ɗaliban ne ranar Alhamis a ƙaramar hukumar Otukpo yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa jihar Enugu, a cewar rundunar 'yan sandan jihar.
Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Benue Sewuese Anene ya tabbatar wa manema labarai ranar Juma'a cewa ɗaliban, waɗanda ke cikin motocin bas guda biyu, sun faɗa hannun 'yan bindiga ne a ranar Alhamis da maraice.
Ya ƙara da cewa ɗaliban sun taso ne daga birnin Jos na jihar Filato a kan hanyarsu ta halartar wani taro a Enugu.
“Ba zan iya faɗa muku jami'ar da ɗaliban suka fito ba, amma dai ɗaliban kiwon lafiya ne da ke kan hanyarsu ta yin balaguro. Ba ni da cikakken bayani a kan yadda lamarin ya faru, amma ina tabbatar muku cewa tuni muka soma gudanar da bincike kan lamarin," in ji Sewuese Anene.
Satar mutane domin karɓar kuɗin fansa wani abu ne da ya yi ƙamari a Nijeriya, inda 'yan bindiga kan sace mutane a gidajensu da gonaki a wasu lokutan ma har da makarantu.