Hukumomi a Burkina Faso sun ce 'yan bindiga sun kashe farar-hula akalla arba'in da biyar a hare-haren da suka kai wasu kauyuka na kasar.
Gwamnan lardin Sahel, Rodolphe Sorgho, wanda ya bayyana hakan ranar Asabar, ya ce an kai hare-haren ne a kauyukan Kourakou na Tondobi na arewa maso gabashin kasar da ke kan iyaka da Jamhuriyar Nijar.
Ya bayyana hare-haren a matsayin "abubuwan takaici da dabbanci" yana mai cewa an kai su ne ranar Alhamis da tsakar dare.
Sorgho ya ce an kashe mutum 31 a Kourakou yayin da mutum 13 suka mutu a Tondobi, yana mai cewa akwai yiwuwar alkaluman wadanda suka mutu su karu.
Gwamnan ya ce martanin da sojoji suka yi ne "ya dakatar da hare-haren 'yan ta'addan".
Ya jaddada cewa suna daukar matakan shawo kan irin wadannan hare-hare da suka addabi yankin.
An kai tagwayen hare-haren ne a kusa da garin Seytenga, inda 'yan bindiga suka kashe akalla farar-hula 86 a watan Yunin da ya gabata.