Gwamnatin Benue da ke tsakiyar Nijeriya ta ce mutum aƙalla 30 ne suka mutu sakamakon harin da wasu 'yan bindiga suka kai ranar Juma'a da daddare a wani ƙauyen na jihar.
Kwamishinan Watsa Labarai na jihar Matthew Aboh ne ya tabbatar da mutuwar mutum 30 a harin da 'yan bindiga suka kai a ƙauyen Ayati.
Sai dai wasu rahotanni sun ce waɗanda aka kashe za su kai 50.
Jihar Benue na fama da ƙarin hare-haren 'yan bindiga a baya bayan nan, waɗanda ake alaƙantawa da makiyaya.
A watan jiya, wani hari da 'yan bindiga suka kai a jihar ya yi sanadin mutuwar aƙalla mutum 25.
Nijeriya ta daɗe tana fama da hare-haren 'yan bindiga da na ƙungiyoyin 'yan ta'adda irin su Boko Haram da ISWAP.
AA