'Yan bindiga sun kashe akalla mutum 20 a wani kauye na Jumhuriyar Afirka ta Tsakiya

'Yan bindiga sun kashe akalla mutum 20 a wani kauye na Jumhuriyar Afirka ta Tsakiya

Maharan sun ƙona gidaje a ƙauyen inda mafiya yawan mazaunansa suka gudu.
Rikicin Jumhuriyar Afirka ta Tsakiya ya ki ci da cinyewa / Hoto: AP

Akalla mazauna wani ƙauye 21 da suka hada da yara ƙanana ne suka rasa rayukansu sakamakon harin da 'yan tawaye suka kaiwa shingen binciken ababan hawa a arewacin Jumhuriyar Afirka ta Tsakiya, kamar yadda mahukuntan kasar suka bayyana.

"'Yan tawayen sun fara kai hari shingen binciken ababan hawa na sojoji, inda suka kashe jami'i daya tare da jikkata wasu da dama, kafin daga bisani su kai hari kan fafaren hula, tare da kashe mutum 20," in ji Ernest Bonang, dan majalisar tarayya mai wakiltar Nzakoundou, kauyen da aka kai wa hari a ranar Alhamis.

Bonang ya ce maharan sun ƙona gidajen ƙauyen, wanda kusan dukkan jama'arsa suka gudu.

Tun 2013 ne Jumhuriyar Afirka ta Tsakiya da ke dimbin arzikin albarkatun kasa na fuskantar rikicin kabilanci tun 2013.

Iyalai sun rasa matsugunansu

Majalisar Dinkin Duniya, wadda ke aikin wanzar da zaman lafiya, ta yi hasashen rikicin ya yi ajalin dubunnan mutane tare da raba sama da miliyan guda da matsugunansu, kaso daya cikin biyar na jama'ar kasar baki daya.

Babu wani da ya dauki alhakin kai harin, amma akwai kungiyoyin 'yan tawaye da dama da ke rikici a arewacin Jumhuriyar Afirka ta Tsakiya.

"'Yan tawayen sun taba mayar da garinmu makwararar jini," in ji Joseph Helari, magajin garin Ndim. "A yau iyalai da dama sun ras agidajensu, kuma sun yi kaura sabod akone gudajen da aka yi."

Helari ya kuma bukaci mahukunta da su kara zage dantse wajen ganin kawo karshen rikici a arewacin Jumhuriyar Afirka ta Tsakiya inda 'yan tawaye suke cin karensu babu babbaka tare da bijirewa kokarin tabbatar da tsaro na Shugaban Kasa Faustin Archange Touade.

TRT Afrika