Mutanen birnin Moscow sun karrama sojojin haya na Wagner da aka kashe a Mali. / Hoto: Reuters         

Mai magana da yawun 'yan aware na Abzinawa a Mali ya ce babu wani taimako daga ƙasar waje da aka samu a yakin da aka fafata a ƙarshen watan Yuli wanda ya haifar da mummunar illa ga dakarun sojojin Mali da ƙawayenta na Wagner, kazalika ba ta samu wani taimako daga Ukraine ba.

A farkon watan Agusta ne 'yan awaren daga arewacin Mali suka bayyana cewa sun kashe aƙalla sojojin Wagner ta Rasha guda 84 da kuma sojojin Mali 47 a wani ƙazamin yaƙi da aka kwashe lokaci ana fafatawa a garin Tinzauaten da ke kusa da kan iyakar Aljeriya.

Matakin dai na zama shan kaye mafi muni da rundunar sojojin haya ta Rasha ta Wagner ta taba fuskanta tun bayan da ta shigowarta ƙasar wadda ke yankin Afirka ta Yamma don taimaka wa sojojin kasar yakar ƙungiyoyi masu tayar da ƙayar baya shekaru biyu da suka wuce.

A martanin da ya yi a ranar 29 ga watan Yuli, mai magana da yawun hukumar leƙen asirin Ukraine ya ce, manufar Mali ita ce Ukraine ta samar wa 'yan awaren bayanai gabanin soma yakin.

Bayan wasu 'yan kwanaki ne, Mali ta sanar da cewa za ta yanke hulɗar diflomasiyya da Ukraine saboda kalamanta.

Babu Shaida

A wata sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen Ukraine ta fitar, ta ce an yi gaggawar ɗaukar matakin, sannan babu wata shaida da ta nuna cewa Kyiv ta taka wata rawa a yaƙin da aka gwabza.

Daga baya ne ita ma Nijar makwabciyarta ta yanke hulɗa da Ukraine, saboda irin waɗannan kalamai.

''Za mu iya fito wa fili mu ce ba mu samu wani taimako daga waje ba a yakin da aka fafata a Tinzaouaten,'' kamar yadda Mohamed Elmaouloud Ramadane na ƙungiyar ƙawancen tsare-tsaren zaman lafiya da tsaro da kuma ci gaba ta dindindin (CSP-PSD) ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters a ranar Laraba.

Da aka tambaye shi ko a baya Ukraine ta taɓa taimaka wa ƙungiyar 'yan tawayen da kuɗi ko kuma horo, sai Ramadane ya ce ''A'a ba mu samu wani taimako daga Ukraine ba.''

Asara mai yawa

Har yanzu dai Mali da Wagner ba su bayyana adadin sojojin da suka rasa a yakin ba, ko da yake a wata sanarwa da ba kasafai take fitarwa ba, a ranar 29 ga watan Yuli Wagner ta ce ta samu asara mai yawa.

Kazalika hukumomin ƙasar Mali suma sun tabbatar da samun asara mai yawa a yaƙin ba tare da bayar da wani adadi ba.

Ƙungiyar Al-Qaeda reshen Jama'a Nusrat al-Islam wa al-Muslimin (JNIM) ta yi ikirarin cewa ta kashe sojojin haya 50 na Wagner da sojojin Mali 10 a wani harin kwanton ɓauna da suka kai a yankin a lokacin.

Majiyoyin tsaro biyu sun ce 'yan awaren da JNIM sun kai wa ayarin motocin sojojin Mali hari a wani daji, amma ba a sani ko ƙungiyoyin biyu suna da wani haɗin kai mai ƙarfi ba.

Yarjejeniyar zaman lafiya

A shekarar 2012 ne 'yan aware na Abzinawa suka ƙaddamar da tawaye kan gwamnatin Mali amma daga baya kungiyoyin 'yan ta'adda masu alaƙa da al-Qaeda da kuma kungiyar ta'addanci ta Daesh suka karɓe ta.

'Yan awaren sun rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya da gwamnatin Mali a shekarar 2015, amma ƙungiyar CSP-PSD ta fice daga zaman tattaunawar a karshen shekarar 2022.

Gwamnonin mulkin sojan Mali da Nijar da makwabciyarta Burkina Faso waɗanda duk suka ƙwace mulki tun daga shekarar 2020, tare da alƙawarin kawar da ‘yan ta'addan da suka mamaye yankin Sahel, sun kuma kulla alaƙa ta tsaro da diflomasiyya da Rasha.

Reuters