Janar Yakubu Gowon, wanda ya jagoranci ƙasar wajen yaƙi da ƴan a-waren Biafra daga 1967-70, ya yi gargaɗi cewar "rashin haɗin-kai" na barazana ga ECOWAS. / Hoto: AA

Ɗaya daga cikin shugabannin da suka kafa ƙungiyar raya tattalin arzikin ƙasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) ranar Laraba ya yi kira a cire takunkuman da aka sanya wa ƙasashen da sojoji suka yi juyin mulki gabanin wani muhimmin taro na gaggawa da shugabannin ƙungiyar za su yi.

Ƙungiyar ECOWAS ta faɗa cikin rikici bayan a watan jiya ƙasashen Mali, Burkina Faso da Nijar sun bayyana ficewa daga cikinta.

Kazalika ƙungiyar tana ƙoƙarin shawo kan wani sabon rikicin siyasa da ya ɓarke a Senegal bayan Shugaba Macky Sall ya ɗage zaɓen da ya kamata a gudanar a watan nan na Fabrairu zuwa Disamba.

Tsohon shugaban mulkin sojin Nijeriya Janar Yakubu Gowon, wanda ya jagoranci ƙasar wajen yaƙin basasa da ƴan a-waren Biafra daga 1967-70, ya yi gargaɗi cewar "rashin haɗin-kai" na barazana ga ECOWAS.

Ya yi kira ga shugabannin ƙasashen Yammacin Afirka su duba yiwuwar "cire dukkan takunkuman da aka sanya wa Burkina Faso, Guinea, Mali da Nijar".

A wani taro da ECOWAS ta gudanar a Abuja, Janar Gowon ya yi kira ga shugabannin mulkin sojin Burkina Faso, Mali da Nijar su janye aniyarsu ta ficewa daga ƙungiyar.

Ya roƙe su cewa "Don girman Allah ku dawo."

Ƙasashen uku na cikin waɗanda suka kafa ECOWAS a 1975, amma ƙungiyar ta dakatar da su daga cikinta sakamakon juyin mulkin da sojoji suka yi wa gwamnatocin fararen-hular ƙasashen.

ECOWAS ta sanya takunkumai masu tsauri a kan Mali da Nijar, matakin da ya harzuƙa sojojin da ke mulki.

Ranar Litinin, sojojin da ke mulki a Guinea, waɗanda suka ƙwace mulki a watan Satumba na 2021, sun rusa gwamnatin ƙasar.

Janar Gowon, mai shekara 89, dattijo ne da ake girmamawa a Afirka kuma wasu kafafen watsa labarai sun rawaito cewa ya gana da shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu kafin ya yi kira a cire wa waɗannan ƙasashe takunkumi.

Shugaban majalisar ECOWAS Omar Alieu Touray ya ce Janar Gowon ya gabatar da "saƙo mai girma".

Touray ya tabbatar da cewa za a gudanar da taro na musamman na ƙugiyar ranar Asabar inda ya ƙara da cewa "shugabanninta za su yi nazari kan saƙonka yayin tattaunawarsu".

AFP