Daraktan cibiyar Africa CDC Dr Ahmed Ogwell, ya ce sahihiyar hanyar shawo kan barkewar annobar ita ce samun damar kutsawa cikin al’ummomi/Photo AA

Daga Coletta Wanjohi

Ranar 11 ga wata Janairu, Uganda ta ayyana cewa ta kawo karshen annobar cutar Ebola, lamarin da ya kawo wa nahiyar Afirka saukin bala’in da cutar ta saka ta a ciki tsawon shekaru.

Amma Cibiyar Dakile Cututtuka Masu Yaduwa ta Afirka, (Africa CDA) - wacce ita ce babbar cibiyar lafiya ta nahiyar, ta gargadi kasashe kan kar su yi sakacin da za a sake samun barkewar wata annobar.

A kalla mutum 55 cikin 143 ne suka mutu sakamakon cutar a karo na takwas da aka samu barkewar ta tun shekara ta 2000 a Uganda.

Za a ci gaba da sanya ido kan kasar na tsawon kwana 90 daga ranar da aka ayyana cewa an kawo kareshen annobar.

Kasashen da ke makwabtaka da ita kamar Jamhuriyyar Dimokradiyyar Congo, DRC ma an ayyana cewa ta kawo karshen annobar a ranar 27 ga watan Satumban bara, bayan fama da annobar a karo na 15.

Kasashen Burundi da Kenya da Rwanda da DRC da Sudan ta Kudu da Tanzania duk sun kasance cikin shirin ko ta kwana bayan da Uganda ta sanar da barkewar cutar ranar 20 ga watan Satumban 2022.

Cutar ta kashe kashi 50 cikin 100 na wadanda suka kamu da ita. Ebola na yaduwa ne sakamakon cudanyar da ta shafi ruwan jikin mai dauke da ita kamar gumi da majina da yawu zuwa mai lafiya.

Daga tsakanin shekarar 2013 da 2016, fiye da mutum 11,300 ne suka mutu sakamakon cutar a yankin Afirka ta Yamma, kamar yadda bayanan hukumomi suka nuna.

Wani nau’in cutar da ya bulla daga Sudan wanda aka gaza gano rigakafinsa ne ya yi sanadin yawancin mace-macen da aka samu din.

Daya nau’in cutar kuma wanda ba shi da tsanani sosai mai suna Ebola Zaire, ya yi sanadin annobar da aka yi ta samu a baya-bayan nan a DRC da ma wasu wuraren.

Bin tsari na da muhimmanci

Hukumar Africa CDC ta ce watakila karshen annobar kawai aka kawo, amma ba a kawar da kwayar cutar ba/Photo AA

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO, ta ce an ware kusan dala miliyan uku don taimaka wa Afirka ta Yamma yaki da annobar da ka iya barkewa a nan gaba.

Kazalika, daraktan rikon kwarya na cibiyar Africa CDC, Dr Ahmed Ogwell, ya jaddada cewa sahihiyar hanyar shawo kan barkewar annobar ita ce samun damar kutsawa cikin al’ummomi.

“Idan ka samu damar shiga cikin al’umma 100 bisa 100, za ka samu damar sanin halin da ake ciki akai- akai, tare da sa idanu da kuma duba kan sakamakon da hakan ke bayarwa,” Ogwell ya fada a yayin wani taron manema labarai.

“Akwai kalubale a tattare da hakan a DRC, musamman a yankunan da ake fama da rikici, wannan dalili ya sa yin hakan na da wahala a wannan yanki na Afirka.”

Ya kara da cewa hadin kai da tsari na da matukar muhimmanci a matakin kasa.

“A duk lokacin da aka samu wani rikici, to akwai yiwuwar a samu mafita ko taimako. Amma idan har ba a yi komai bisa tsari ba, to ba za a samu sakamako mai kyau ba.

"A Uganda, bin tsarin ya faro ne tun daga ranar farko, ministar lafiya ce ke jagorantar komai, kuma ta tsara komai har zuwa ranar da aka kawo karshen annobar.”

Hukumar Africa CDC ta ce watakila karshen annobar kawai aka kawo, amma ba a kawar da kwayar cutar ba.

Jiran rigakafi

A shekarar 2019, Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Amurka ta amince da Ervebo, wanda ta ce ba shi da illa kuma kariya ne ga cutar Ebola nau’in Zaire da ta fi yaduwa a DRC.

Amma har yanzu ba a samu rigakafin cutar nau’in Sudan ba wadda ta dade tana addabar Uganda.

Haka kuma har yanzu ba a gano asalin cutar ba, sai dai ana ci gaba da bincike a kanta.

Uganda na shirin fara gwajin rigakafin Ebola nau’in Sudan din a kan mutane. A watan Disamban 2022 aka shigar da kashi na farko na rigakafin cikin kasar.

Dr Ogwell y ace idan ana so a hana barkewar annobar a nan gaba, dole ne ‘yan kasa su dinga bayar da bayanai.

“Annoba kan fara yaduwa ne kuma takan kare ne a cikin al’umma. Idan har a cikin al’umma annobar ta barke, to za a iya saninta nan da nan.

“Idan kuwa al’umma bas u gane barkewar annoba ba ko kuma suka ki fada, to ta fi saurin yaduwa a tsakanin mutane,” in ji Ogwell.

Ana jinjina wa Uganda kan saurin gano cutar da take yi da kuma samar da magani don dakile yaduwarta.

TRT Afrika