Shugaban tawagar dakarun RSF a Sudan Omar Hamdan Ahmed ya yi magana a taron manema labarai a Nairobin Kenya. Hoto / Reuters  

Dakarun rundunar ɗaukin gaggawa ta RSF a Sudan sun ce a shirye suke su koma kan teburin tattaunawa da gwamnati "idan har akwai muhimman tsare-tsare da aka tanadar."

Rundunar ta bayyana hakan ne a ranar Litinin a yayin wani taron manema labarai a birnin Nairobi na ƙasar Kenya ta bakin Birgediya Janar Omar Hamdan, shugaban tawagar shiga tsakani ta RSF.

A watan Mayun 2023 wakilan masu shiga tsakanin daga Saudiyya da Amurka suka gudanar da wani zaman tattaunawa a Jeddah tsakanin wakilan Sojojin Sudan da RSF.

An cim ma matsaya a zaman tattaunawar, inda ɓangarorin biyu suka yi alƙawarin kaucewa ayyukan soji da ka iya cutar da fararen-hula, tare da jaddada muhimmancin kare fararen-hula da bin dokokin kare hakkin bil'adama na ƙasa da ƙasa.

'Komawa teburin tattaunawa'

"RSF ba ta ƙi amincewa da hanyoyin zaman lafiya kwata-kwata ba," in ji Hamdan. "A shirye muke mu koma teburin tattaunawa idan har akwai ingantattun tsare-tsare a wannan fanni."

Kawo yanzu dai babu wani bayani a hukumance daga ɓangaren hukumomin Sudan.

Kalaman Hamdan na zuwa ne bayan Rasha ta ƙi amincewa da wani daftarin kwamitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya a ranar Litinin wanda ya buƙaci sojojin Sudan da RSF su cika alƙawuransu ƙarƙashin yarjejeniyar Jeddah.

Da farko dai, daftarin wanda Birtaniya da Saliyo suka gabatar, ya samu amincewar sauran ƙasashe 14 na kwamitin sulhun MDD.

Kare fararen-hula

Mataimakin jakadan Rasha a MDD, Dmitry Polyanskiy, ya ce babban jigon daftarin shi ne rashin bayyana wanda ke da alhaki kan batutuwan da suka shafi kare fararen-hula da kuma kare kan iyakoki.

Kazalika ya soki Birtaniya da "kaucewa yin magana kai-tsaye ga halattacciyar gwamnatin Sudan a matsayin wadda ke da alhaki," lamarin da ya ce ba za a amince da shi ba.

Tun daga tsakiyar watan Afrilun 2023, yaƙi ya ɓarke tsakanin sojojin Sudan da dakarun RSF wanda ya yi sanadin mutuwar mutane fiye da 20,000 tare da raba fiye da mutum miliyan 11 da muhallansu, a cewar MDD.

Ana ƙara samun kiraye-kiraye daga ƙasashen duniya kan a kawo ƙarshen wannan yaƙi, wanda ya jafe miliyoyin mutane cikin yunwa da mutuwa sakamakon tsananin ƙarancin abinci a jihohi 13 cikin 18 na Sudan.

AFP