Sama da mutum 12,000 aka kashe inda kuma aka raunata sama da 33,000 a wannan yakin. / Hoto: Reuters

Daga Coletta Wanjohi

Irin mugun yakin da ake yi tsakanin sojojin Sudan da kuma rudunar RSF tun daga Afrilun 2023 ya ci gaba har cikin sabuwar shekarar 2024, inda Sudan din ta yi wa jakadanta da ke Kenya kiranye sakamakon abin da ta kira karbar da kasar ta yi wa abokin adawarsu Mohamed Hamdan Dagalo babban kwamandan RSF.

Duk da cewa Kenya ta yi karin haske kan cewa tattaunawar da aka yi tsakanin Shugaba William Ruto da Dagalo a ranar 3 ga watan Janairu an yi ta ne domin kara tabbatar da zaman lafiya a Sudan, sai dai gwamnatin mulkin Sudan din na kallon lamarin a matsayin cin mutunci.

Wannan matsalar ta diflomasiyya ta faru ne tun bayan Dagalo ya soma wani shiri na zuwa kasashe bayan sama da mutum 12,000 suka rasu inda aka raunata sama da mutum 33,000. Majalisar Dinkin Duniya ta ce mutum miliyan 6.6 sun rasa muhallansu.

Shekarar bakin ciki

A farkon 2023, 'yan Sudan ba su san cewa kasarsu za ta fada cikin yaki bayan wata hudu da shiga sabuwar shekarar ba.

Sai dai abin mamakin, jam'iyyu biyun da suka yi aiki tare domin hambarar da gwamnatin Omar al-Bashir su ne suka rinka yaki da juna.

Sudan ta yi wa jakadanta na Kenya kiranye bayan ziyarar da Mohamed Dagalo ya kai kasar. / Hoto: Reuters

Yakin da ya barke tsakanin RSF da sojojin Sudan ya kawar da duk wata fata da ake da ita na zabar sabuwar gwamnati a shekara biyu, karkashin yarjejeniyar da aka cimmawa a 2022 tsakanin sojojin kasar da kuma jam'iyyu.

Tun daga lokacin, an ta samun bala'o'i a Sudan, wadda ita ce kasa ta uku mafi girma a Afirka mai mutum miliyan 48.

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa jama'ar kasar na matukar bukatar taimako sakamakon wannan yakin.

Zuwa Disambar 2023, sama da mutum miliyan 6.6 suka rasa muhallansua ciki da wajen kasar. Sai da kasashen Chadi da Masar da Sudan ta Kudu masu makwaftaka suka rinka bayar da taimako ga 'yan Sudan din da ke guduwa saboda yakin.

Duka janarorin biyu masu rikici da juna ba su tabuka wani abin a zo a gani ba da zai iya kawo karshen wannan yakin, duk da lamarin yana kara tabarbarewa a kullum. Kokarin da aka rinka yi na shiga tsakanin bangarorin biyu bai haifar da wata mafita ba.

"Da sojojin Sudan din da RSF din na takama da karfi inda duka suke ganin kamar za su iya magance matsalolinsiu ta hanyar yaki," in ji Dakta Edward Githua, wanda kwararre ne ta bangaren harkokin kasashen waje a tattaunawarsa da TRT Afrika.

Janar Burhan na daga cikin jagororin juyin mulkin da ya hamabar da gwamnatin Omar al-Bashir. / Hoto: Others

Kusan mutum miliyan 17.7 a fadin Sudan, wanda adadin ya kai kaso 37 a cikin 100 ke fuskantar karancin abinci tsakanin Oktobar 2023 zuwa Fabrairun 2023," kamar yadda wata hukumar Majalisar Dinkin Duniya ta FAO ta bayyana a wani sabon rahoto.

"Akasarin jama'ar da ke fama da tsananin karancin abinci na zaune ne a jihohin da yakin ya shafa, daga ciki har da Darfur da Greater Kordofan da Khartoum - da Bahri da Omdurman.

Rahoton na FAO ya kuma ruwaito cewa ana ta aikata sace-sace a kasuwanni da bankuna da masana'antu da kuma gine-ginen gwamnati.

Bukatar sake kallon lamarin

Kungiyar Tarayyar Afirka (AU) ta dage cewa wani shiri da Sudan ke jagoranta shi ne mafita daya tilo daga cikin halin da ake ciki.

A taron koli na 41 na kungiyar IGAD, wanda Sudan ta kasance mamba, an ba da muhimmanci kan "tsarin shiga tsakani na bai daya da kasashen Afirka suka kulla". Bangarorin da ke fada da juna sun tabbatar wa kungiyar yankin cewa za su ba da damar tattaunawa.

Janar al-Burhan ya kuduri aniyar "tsagaita wuta ba tare da wani sharadi ba" da warware rikici ta hanyar tattaunawa ta siyasa, gami da ganawa gaba da gaba da kwamandan RSF wanda IGAD ta taimaka. An ce Dagalo ya amince da wannan kudiri.

A halin yanzu wajibi ne IGAD ta gaggauta gudanar da shawarwarin da Sudan za ta jagoranta, wadda za ta kai ga kafa gwamnatin rikon kwarya karkashin jagorancin farar hula, daga baya kuma, za a gudanar da zabukan dimokuradiyya.

Amma ko janar-janar din za su girmama waɗannan alkawuran? Ya zuwa yanzu, an samu dan ci gaba kan wannan makin.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce wannan yakin ya raba 'yan Sudan miliyan 6.6 da muhallansu. / Hioto: Others

"Wani abu daya da yake a bayyane shi ne jama'ar Sudan na son mulkin Dimokuradiyya," kamar yadda manzo na musamman na Majalisar Dinkin Duniya a Yemen, Jamal Benomar ya shaida wa TRT Afrika.

Takunkumai ba su yi wani tasiri ba. A watan Yunin shekarar da ta gabata ne Amurka ta kakaba takunkumi kan kamfanonin da ta zarga da rura wutar rikicin Sudan, biyu daga cikinsu mallakin kwamandan RSF Dagalo ne da 'yan uwansa.

A watan Satumba, Amurka ta saka takunkumai kan tsohon ministan harkokin wajen Sudan Ali Karti da wasu kamfanoni biyu inda ake zarginsu da hannu wurin kawo cikas ga zaman lafiya da tsaron Sudan.

Daga baya a cikin watan, ta sanar da wasu takunkumai kan mataimakin shugaban RSF Abdelrahim Dagalo kan zargin take hakkin bil adama.

"Akwai bukatar kasashen duniya su kara kaimi. Wannan ita ce hanya daya tilo. Amincewa da su (bangarorin da ke rikici), kamar yadda suka yi a baya, bai yi tasiri ba. Lokaci yayi don sabon tsarin," kamar yadda Benomar ya bayyana.

TRT Afrika