Masu halartar taruka ko wasa su kan mayar da hankalinsu kan daukar hoton abin da ke faruwa a wayoyinsu maimakon mayar da hankalinsu kacokan kan taron ko wasan. Hoto: Reuters

Daga Mazhun Idris

Da dadewa tun kafin daukar hotuna ya zama ruwan dare da kuma salon daukar hoto na selfie, akwai wani abu da ake kira "mayar da hankalinka kacokan kan abin da ke faruwa a lokacin".

Wasu hotuna biyu da aka hade wuri guda wadanda kafar yada labarai ta ESPN ta wallafa a shafinta na Twitter @SportsCenter a ranar 23 ga watan Yuli, kwana biyu bayan shahararren dan wasan kwallon kafa Lionel Messi ya fara taka leda a kungiyar Inter Miami ta Amurka, hotunan sun yi kokarin bayar da labari.

A hoton farko, Messi ya durkusa, da alama yana cikin wasa yana tunanin abin da zai yi na gaba. Daga dama kuma a gaban 'yan kallo shi ne tsohon dan wasan Ingila David Beckham yana zaune yana kallon wasa. Sauran 'yan kallo suna zaune a kasa da yawansu — ciki har da matar Beckham, Victoria — suna daukar hotunan abin da ke faruwa a wayoyinsu.

Hoto na biyu shi ne na shahararren dan wasan kwallon kwando LeBron James, ana gab da zura kwallo a raga. An yi amfani da waya an dauko hoton 'yan kwallo kuma an jiyo ana cewa latsa-latsa, yayin da aka yanko wani hoto karami daga babba wanda yake nuna fuskar wani dattijo mai kallon wasa yana kallon muhimman abubuwan da ke faruwa a wasan da idonsa a tsanake.

Beckham da wani jami'i a gasar kwallon kwando ta Amurka (NBA) suna daga cikin mutane 'yan kalilan daga cikin dimbin mutane da hankalinsu ya koma kan daukar abin da ke faruwa a wayoyinsu, madadin su mayar hankalinsu kan abin da ke faruwa.

Doka Muhsin Ibrahim, wani masani ne kan yada labarai da sadarwa a Cibiyar Nazari kan Afirka a Jami'ar Cologne da ke kasar Jamus, ya ce yana kallon abin a matsayin wani abu mara tsari, inda mutum yake yawo da hankalinsa daga wani abu zuwa wani.

Wasu mahalarta taro suna kokarin jin dadin kallon abin da ke faruwa da kuma daukar abin a wayarsu a lokaci guda. Hoto: Reuters

"Ci gaba da samun yawan wayoyin hannu yana cutar da zamantakewarmu. Saboda wayoyin hannu, muna ganin wasu sabbin al'adu na zamani ba kakkautawa," kamar yadda ya shaida wa TRT Afrika.

Nishadin yanzu-yanzu

Kamar yadda shafin intanet na MTV ya bayyana, shahararriyar mawakiyar nan 'yar Birtaniya Adele ta taba bai wa wani magoyin bayanta shawara yayin da yake daukar hoton wasanta a shekarar 2016 bayan ya mayar da hankalinsa a kan waya maimakon wasan da ake yi, bayan ya biya kudi ya kalli wasan.

"Ba ka butakar ka kalla ta wayarka. Ina nan yanzu haka. Ina so ka ji dadin kallon wasana, saboda akwai mutane da yawa a waje wadanda ba su samu damar shigowa ciki ba," in ji ta, wannan ya jawo ka-ce-na-ce kan abin da za ka iya yi da wanda ba za ka iya yi ba idan ka halarci wasan Adele.

A yayin taruka, da wuya kake ganin masu halarta sun natsu cikin farin ciki su mayar da hankali kacokan kan abin da ke faruwa.

Yawancin su za ka ga sun rike wayoyin hannu, inda suka raba hankalinsu biyu daga abin da ke faruwa.

Shin me ya sa mutane da saninsu suke raba hankalinsu su rika amfani da wayarsu ana tsakiyar wani abu mai dadi?

Huzaifa Baraya, dalibi ne a fannin injiniyan na'u'rori a Jami'ar Ahmadu Bello ta Zariya, ya ce ana daukar abu a waya ne saboda adana tarihin kyawawan abubuwan da suka faru.

"Bayan daukar hoton irin wadannan abubuwa ina tura wa 'yan uwa da abokanan arziki ne kuma sai na wallafa a shafukan sada zumuntana," kamar yadda ya shaida wa TRT Afrika.

Da aka tambaye shi ko yana tuna ya yi amfani da hotuna da bidiyo da ya ajiye a wayarsa, sai Huzaifa ya ce, "Ina yi kuma a wasu lokuta ma ina sake wallafa tsofaffin hotuna wadanda na dauka watanni ko shekaru da suka wuce, a matsayin tuna baya ga wani abin farin ciki da ya faru."

Son tara dimbin abubuwa a waya

Duk da ci gaban da aka samu sosai ta bangaren daukar hotuna na zamani, cikin sauki muke yada muhimman abubuwa da suka faru da mu ga 'yan uwa da abokan arziki, masu nazari kan kafofin yada labarai na zamani sun nuna matukar damuwa dangane da wannan dabi'a.

Yawancin masu halartar taruka suna daukar hoton abin da ke faruwa saboda su sanya a shafukan sada zumunta. Hoto:Reuters

"Gaba daya wayoyin hannu suna bata zamantakewar ta yadda take bata shakuwar sanadin hulda da juna da fallasa sirrinmu da hana mu lokacin iyalinmu," in ji Dokta Muhsin.

Idan mutane kamar Huzaifa suna sake amfani da tsofaffin hotuna da bidiyo ta hanyar tuna ba, to akwai wasu irinsu Muhammad Kamil, dalibi da ke nazari kan kimiyyar tattara bayanai da dakin karatu, wanda ya ce yana ajiye hotuna da bidiyo ne kawai ba da niyyar sake amfani da su ko wallafa su ba nan gaba.

Kamil ya ce yana amfani da kaso 10 cikin 100 ne kawai na hotuna da bidiyo da ya ajiye a wayarsa — sauran kawai yana ajiye da su ne kawai, wata kila ma ba za ka taba amfani da su ba.

A daya bangaren kuma akwai Aisha, wacce daliba ce a fannin nazarin shugabanci wadda ta ce tana amfani "da kusan kaso 80 cikin 100" na abubuwan da ta ajiye a wayarta, duk da dai ta ce ta fi so ta mayar da hankalinta kacokan kan abin da ke faruwa a gabanta, maimakon daukar hoton abin da ke faruwa da wayarta.

Wannan ya kawo mu da magana kan matsalar nan ta son tara dimbin abubuwa a ma'ajiyar wayarmu.

Wayoyinmu sun kunshi hotuna da bidiyo da muka dauka da kuma wadanda suka sauke daga intanet. Kama daga kade-kade da fina-finai zuwa zayyane-zayyane da kuma sauran bayanan intanet.

Shakka babu kamfanonin da ke kera wayoyi suka tallata ingancin hoto da kyamara idan suna tallace-tallacen sababbin wayoyi. Wannan yana da alaka da yadda muka raja'a daukar hotuna da ajiye su a kan wayoyinmu.

Kamar yadda ake cewa a wannan lokaci da waya ta zama ruwan dare — mayar da hankalin kacokan kan abin da ke faruwa, amma kada ka bari a bar ka a baya wajen daukar hoton shi.

TRT Afrika