Rundunar ta ce an kashe sojoji uku a harin, kuma a halin yanzu sojojin na ƙokarin kakkaɓe sauran 'yan ta’adda da ka iya kasancewa kusa da wurin inda suke bi lungu da saƙo suna nemansu. ./Hoto: Rundunar  Sojin Nijeriya

Rundunar sojin Nijeriya ta yi ƙarin haske game da yadda dakarunta suka kashe mayaƙan ƙungiyar ISWAP 12 bayan 'yan ta’addan sun kai wa sojojin farmaki da safiyar Litinin.

Wata sanarwa da rundunar sojin Nijeriya ta fitar ranar Laraba ta bayyana cewa mayaƙan ISWAP ɗin sun far wa wani sansanin sojojin rundunar Operation Hadin Kai ne a garin Kukawa da ke ƙaramar hukumar Kukawa ta jihar Borno.

“Mayaƙan sun yi ƙoƙarin kutsawa cikin sansanin sojojin ta hanyar amfani da mota mai ɗauke da bam, sai dai kuma dakarun Nijeriya sun mayar da martani tare da tallafawar sojojin sama da kuma jirage mara matuƙa,” in ji sanarwar da rundunar sojin Nijeriya ta wallafa a shafinta na X.

“Martanin ya tilasta wa 'yan ta’addan ja da baya a firgice inda suka bar waɗanda aka kashe a cikinsu a baya. A lokacin fafatawar, an kashe 'yan ta’adda 12 sannan da dama daga cikinsu sun gudu ɗauke da raunuka,” in ji sanarwar.

Sanarwar ta ƙara da cewa ababen da aka samu daga 'yan ta’addan da suka tsere sun haɗa da bindigogi ƙirar AK-47 biyar, gurnetin roka ɗaya, bindigogin harbin jirage biyu da kuma babura 40.

Sai dai kuma rundunar ta ce an kashe sojoji uku a harin, kuma a halin yanzu sojojin na ƙokarin kakkaɓe sauran 'yan ta’adda da ka iya kasancewa kusa da wurin inda suke bi lungu da saƙo suna nemansu.

Kazalika babban hafsan rundunar sojin ƙasa ta Nijeriya Laftanar Janar Olufemi Oluyede ya jinjina wa sojojin game da jajircewarsu yana mai kira a gare su su ci gaba da fatattakar 'yan taddan.

TRT Afrika da abokan hulda