Rufe sararin samaniyar Nijar zai shafi sufurin jiragen sama a Yammacin Afirka. Hoto/Niger Airlines

Dangantaka tsakanin Jamhuriyar Nijar da kungiyar ECOWAS da wasu kasashen Yamma na kara kazanta sakamakon kifar da gwamnatin Mohamed Bazoum da sojoji suka yi, lamarin da ake fargabar zai iya jefa yankin Sahel cikin karin rikici.

A ranar Lahadi da dare ne sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar suka sanar da rufe sararin samaniyar kasar, abin da ke nufin jirage ba za su iya shawagi ko kuma wucewa ta Nijar ba.

Sun dauki matakin ne bayan sun yi zargin cewa kugiyar raya tattalin arzikin kasashen Yammacin Afirka, ECOWAS, na shirin kai wa kasarsu hari bayan wa'adin da ta ba su na mayar da Bazoum kan mulki ko su fuskanci karfin soji ya wuce.

Ana fargabar rufe sararin samaniyar za ta sa jirage su rinka yin zagaye lamarin da zai iya haifar musu da sabbin kalubale.

Masana sufurin jiragen sama sun bayyana yadda suke ganin rufe sararin samaniyar na Nijar zai shafi wasu daga cikin kasashen Yammacin Afirka da ita kan ta Nijar.

‘Karin zagaye’

Keftin Rabiu Yadudu, wani mai sharhi kan harkokin sufurin jiragen sama a Nijeriya, ya shaida wa TRT Afrika cewa abu na farko da rufe sararin samaniyar zai jawo shi ne zagaye, inda ya ce a halin yanzu ya zama dole jiragen da suka saba bi ta Nijar su zagaya ta wata kasa domin zuwa inda za su.

“Dole jirgin da ya saba bi ta Nijar ya yi zagaye wanda zai sa ya tsallaka karin kasashe sannan nisan tafiyar zai karu,” in ji shi. Ya bayyana cewa yanayin yadda jirgi yake, ya fi son bin hanya mikakkiya a maimakon ya yi ta zagaye-zagaye.

Karin tsada a sufurin jiragen sama

Keftin Yadudu ya kara da cewa irin wannan zagaye da jirage za su rinka yi sakamakon rufe sararin samaniyar Nijar, zai kara tsada a harkar sufurin jiragen sama.

“Wannan zagaye zai jawo karin nisan hanya da karin dadewa a sama da karin kashe kudi wurin shan mai da kuma karin biye-biyen kudi na haraji da ake biyan kasashen da ake bi ta samansu.

“Hakika wannan zai kawo karin tsada a harkar jiragen sama amma ba zai jawo a hana sufurin ba,” in ji Keftin Yadudu.

A halin yanzu ana fuskantar tsadar tikitin jiragen sama inda ko a Nijeriya ana kashe sama da dala 100 a tafiyar cikin gida, sama da dala dubu a tafiya zuwa wasu kasashe.

Asarar kudin shiga ga Nijar

Baya ga tsada a sufurin jiragen sama, ita kanta Nijar za ta rinka tafka asara sakamakon rufe sararin samaniyarta, kamar yadda Abba Isma’il, mai sharhi kan lamuran yau da kullum ya shaida wa TRT Afrika.

“Su kuma abin zai shafe su saboda akwai kudin da suke samu idan jirgin sama ya ratsa sararin samaniyarsu, ita Nijar za ta yi wannan asarar wadanda kudade abin da ke nufin asarar ta zama hanya biyu,” in ji shi.

Akasarin jiragen da za suka fito daga Turai ko kuma suka tsallako Bahar Rum kuma suka nufi Nijeriya ko Kamaru ko Jamhuriyar Benin da wasu kasashen Yammacin Afirka, suna ratsawa ne ta Nijar.

Makalewar ‘yan kasashen waje a Nijar

Akwai jama’a da dama daga kasashe daban-daban na duniya da ke zaune a Nijar ko dai don kasuwanci ko aiki ko kuma zama na na din-din-din.

Tuni Faransa da wasu kasashen Turai suka soma kwashe ‘ya’yansu daga kasar domin gudun abubuwan da ka iya zuwa su dawo.

Sai dai abin da ake fargaba shi ne a halin yanzu bayan rufe sararin samaniyar Nijar akwai jama’a da dama wadanda suke so su koma kasashensu amma babu damar hakan.

“Duk wasu baki da suke kasar da kuma ‘yan makaranta da suke karatu da mazauna kasar wadanda ba ‘yan kasa ba, su ma hakan zai shafe,” in ji Abba Isma’il.

Wani abu makamancin haka ya faru a Sudan inda bayan rufe sararin samaniyar kasar sai da aka sha matukar wahala kafin a kwaso jama’ar wasu kasashe daga can har da ‘yan Nijeriya.

Yakin Sudan

Yakin da ake yi a Sudan shi ma ya jawo matsaloli da suka shafi sufurin jiragen sama.

Rufe sararin samaniyar da kasar Sudan ta yi ta tilasta wa jiragen sama masu bi ta cikinta yin zagaye, abin da ya jawo cikas sosai.

Alal misali Alhazai daga Nijeriya da Nijar da wasu kasashe sun samu karin farashin kudin jirgin sama a lokacin da suke dab da tafiya aikin Hajji sakamakon zagayen da jiragen suka rinka yi.

Kamfanonin jiragen saman sun bayyana cewa karin mai da jiragen za su sha da kuma nisan tafiya su ne suka haifar da wannan karin.

Haka kuma zagayen da aka rinka yi ya matukar kara awowin da ake shafewa misali daga Nijeriya zuwa Saudiyya.

TRT Afrika