Kasashe masu tasowa na fama da matsalar bayar da gudunmawar jini. Hoto/WHO

Daga Umar Yunus Jos

Jini wani sinadari ne da ke gudana a cikin jikin mutane wanda ke aikin sarrafa iska da sauran sinadarai na abinci, don samar da rayuwa mai inganci.

Duk lokacin da babu jini ko kuma ya yi ƙaranci a jikin mutum, wannan mutumin na cikin garari.

Wannan sinadari, da babu inda ake sarrafa shi sai a cikin jikin ɗan adam, ba a maye shi da komai, sannan ɗan adam ne kaɗai mai samar da shi.

Alƙaluman Hukumar Karɓa Da Adana Jini Ta Nijeriya, National Blood Service Commission (NBSC) na baya-bayan nan, sun nuna cewa, Nijeriya na samun kashi 27% ne kaɗai na jinin da take buƙata daga wajen masu bayar da gudunmawar jini a kowace shekara.

Hakan na nufin, akwai wawakeken giɓi na kimanin kashi 73% da ya kamata a cike kowace shekara, a yunƙurin da ake yi, na samun gudumawar jini daga mutane.

Ana iya samun jini ta wajen masu bayar da gudunmawa bisa raɗin kai, ko masu bayarwa a ba su kuɗi ko kuma ƴan uwa da abokan arziƙin mai buƙatar jini, da suke bayarwa don a maye gurbin wanda aka saka wa ɗan'uwansu.

Mabuƙata jini su ne marasa lafiya da suka rasa jini sakamakon wata cuta da ke ƙone jinin jikin mutum, ko mata lokacin haihuwa, ko waɗanda suka gamu da hatsari suka rasa jini, ko waɗanda rikici ya ritsa da su aka yi musu rauni jini ya zuba sosai, ko kuma waɗanda iftila'i daga Allah ya faɗa musu suka shiga yanayin da suke buƙatar ƙarin jini, da dai sauransu.

A baya, a ƙasashe masu tasowa, kamar ƙasashen Afrika na yamma da sahara kamar Nijeriya, mutane bisa raɗin kansu, suna kai kansu cibiyar karɓa da adana jini ko kuma asibiti, don su bayar da jininsu kyauta ga masu buƙata.

Kafin a amince mutum ya bayar da gudunmawar jininsa, sai an tantance ƙoshin lafiyarsa da kuma ingancin jikinsa, don kauce wa haihuwar guzuma.

Dakta Muhammad Sulaiman na Babban Asibitin Dutse jihar Jigawa, ya ce ƙarancin jini yana da hatsari sosai ga rayuwar ɗan adam, domin idan jini ba ya zagayawa a cikin jiki yadda ya kamata, zai kai ga wasu sassan jiki su mutu, abin da zai sa mutum ya nakasa ko ma ya rasa ransa.

Dakta Muhammad Sulaiman, Malami a Babban Asibitin Dutse a Jihar Jigawa

Sai dai kuma yanzu lamarin bayar da gudunmawar jini bisa raɗin kai yana fuskantar koma baya sakamakon wasu dalilai.

A cewar Dr Muhammad, rashin fahimta da talauci da yaɗuwar cututtuka suna kan gaba gaba wajen kawo wa harkar bayar da gudunmawar jini tarnaƙi.

Da farko, da yawan mutane sun ɗauka idan mutum ya bayar da jini, jininsa zai ragu. Ba su fahimci idan mutum ya bayar da jini shi ma jininsa ƙaruwa zai yi ba.

Dakta Muhammad Sulaiman

Na biyu, talauci da raɗaɗinsa ya sa mutane ba sa ci su ƙoshi ballantana su samu isasshen sinadarin gina jiki da zai ba su lafiyar da za su iya bayar da jini ba tare da damuwa ba.

Na uku akwai yaɗuwar cututtukan zamani da ake ɗaukar su ta hanyar jini, kamar HIV da ciwon hanta da sauransu.

Yawaitar waɗannan cututtukan a tsakanin al'umma, ya sa masu isasshiyar lafiyar da za su iya bayar da gudummawar jini sun yi ƙaranci, idan aka kwatanta da baya," Dr Muhammad ya jaddada.

Har ila yau, bincike ya nuna cewa, al'ada da addini suna taka muhimmiyar rawa wajen mayar da hannun agogo baya a harkar bayar da gudummawar jini.

Wasu al'ummomin suna ganin haramun ne wani ya bayar da jininsa a saka wa wani. Wasu kuma gani suke yi idan aka ɗebi jininsu za a yi tsafi da shi a cutar da su ko waninsu.

Akwai waɗanda suka yi imanin, idan suka bayar da jininsu, za su kamu da rashin lafiya mara magani.

Amma a wajen Emmanuel Toma ɗan shekaru 37 da haihuwa, batun bayar da jini ba shi da nasaba da al'ada ko addini ko jin ƙai; batu ne na ba ni gishiri in ba ka manda.

"Gaskiya ni jinina na sayarwa ne. Idan na karɓi kuɗi, ina sayen abinci mai kyau da zai ba ni lafiya sosai don gobe na iya ba wani.

Ka ga ai mun taimaki juna ko?" inji shi. Nura Alhasan ɗan shekaru 43 da haihuwa, ya shaida wa TRT Afrika cewa, a baya yana bayar da gudummawar jini, amma halin ko in kula da wulaƙanci da wasu jami'an cibiyar bayar da jini da yake zuwa, su suka sa ya dena bayar da gudummawar jini.

A cewarsa, "ma'aikatan ba sa zuwa da wuri kuma ba sa halartar mutane a kan lokaci, hakan ya sa ina makara zuwa wajen aikina. Shi ya sa na dena zuwa cibiyar kwata kwata."

Amma ya ce nan gaba idan ya samu inda ba za a dinga ɓata masa lokaci ba, ko kuma ya fahimci abubuwa sun sauya a waccan cibiyar, zai koma bayar da gudummawar jinin.

Jama'a da dama na sayar da jininsu inda suke amfani da kudin wurin sayen abinci. Hoto/WHO

Akwai cibiyoyin sarrafa jini na ƙasa National Blood Transfusion Service (NBTS), waɗanda gwamnatin tarayyar Najeriya tare da haɗin gwiwar Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta assasa, da hadafin sauƙaƙa karɓa da adana jini don mabuƙata.

Kallamu Abdussalam yana halartar ɗaya daga cikin cibiyoyin, Kuma ya shaida wa TRT Afrika cewa, an ba shi wani katin shedar da ke nuna shi mai bayar da gudummawar jini ne.

Saboda haka, duk lokacin da shi, ko wani nasa na jiki: kamar mata, ko ƴaƴa ko mahaifa suke buƙatar ƙarin jini, za a ba su jini kyauta da zarar ya nuna katin shedar. Saboda haka, in ji Dr Muhammad.

Zaburar da jama'a da wayar musu kai game da muhimmancin bayar da gudunmawar jini, zai ceci rayukan mutane da dama da ke rasa rayukansu sakamakon ƙarancin jini.

"Amfani da kafofin sadarwa na zamani da na gargajiya, musamman a yankunan karkara, zai taimaka matuƙa, wajen fahimtar da ƙarin mutane game da fa'idar da ke tattare da bayar da gudunmawar jini, kamar yadda Dakta Muhammad ya bayyana.

Ya ƙara da cewa, ya kamata mutane su fahimci cewa, don an ɗebi jinin mutum, ba ya nufin nasa ya ragu. Hasali ma, ƙaruwa zai yi, kuma ya ƙara wa mai bayarwan lafiya.

Ya kamata a ƙara adadin cibiyoyin karɓa da adana jini domin su wadata. Sannan a samar musu ƙwararrun ma'aikata da ingantattun kayan aiki.

Ma'aikata a cibiyoyin karɓa da adana jini su dinga samun horo game da sanin makamar aiki akai-akai, don su dinga kyautata mu'amalarsu da masu bayar da gudunmawar jini.

Sannan akwai buƙatar shugabannin addini da sarakunan gargajiya su faɗakar da mabiyansu kan rashin sahihancin camfe camfe da shafi-faɗin da akan yaɗa game da bayar da gudunmawar jini.

Bugu da ƙari, ya kamata gwamnati ta ƙara ƙaimi wajen kyautata rayuwar ƴan ƙasar, ta hanyar bijuro da tsare-tsare da za su rage talauci da samar da aikin yi, da inganta kiwon lafiya da ilimi da kuma haɓaka tattalin arziƙin ƙasa.

Waɗannan matakan za su taimaka wajen kawar da matsalolin da ke hana mutane bayar da gudunmawar jini."

TRT Afrika