Abba Kabir Yusuf ya nuna rashin jin dadinsa kan abin da ya faru tsakaninsa da matar shugaban DSS. Hoto/@Kyusufabba

A karon farko, Gwamnan Jihar Kano da ke arewacin Nijeriya, Abba Kabir Yusuf ya fito ya fito fili ya bayyana rikicin da ya faru tsakaninsa da Aisha Magaji Bichi, matar shugaban hukumar DSS ta Nijeriya kafin zaben kasar na 2023.

A yayin wani taro da malaman addini a Kano, gwamnan ya zargi Aisha Magaji Bichi da zagin iyayensa sannan ta sa jami’an DSS su kama shi.

A cewarsa, lamarin ya faru ne bayan an samu rashin jituwa tsakanin magoya bayansa da kuma jami’an DSS a filin jirgin sama na Mallam Aminu Kano da ke birnin Kano.

Ya ce da ya ga ana samun hatsaniya, sai ya ce bari ya je ya shaida mata abin da ke faruwa.

“Sai na tarar da ‘yan uwansu ‘yan DSS sun fi su talatin da biyar, jibga-jibga, sai na ga daraktansu, na ga wasu manya-manyan mata, ita kuma tana ciki, na ce bari na je na gaya mata abin da yaranta suke yi don a yi musu fada,” in ji gwamnan na Kano.

“Wallahi-Tallahi da wannan abin na shiga wurin nan, ina zuwa na ce Madam kin ga yadda yaranki suke ta dukanmu, amma tana tashi sai ta ce kar ka yi mini rashin mutunci! Wane ne kai? Zan ci mutunci ka,” in ji Abba Kabir Yusuf.

Gwamnan na Kano ya ce lokacin da lamarin ya faru bai wuce wata biyu ba da ya hadu da maigidanta a Abuja inda suka yi wasa da dariya abin da ya sa ya ce bari ya sanar da shi abin da ke faruwa.

Abba Kabir ya ce nan take ya tafi wani wuri ya dauki waya ya kira Yusuf Magaji Bichi sai wani ya dauki wayar ya ce ba ya nan, sai ya bar masa sako cewa ya shaida masa abin da ya faru tsakaninsa da matarsa.

Ya ce bayan ya dawo ya zauna sai ta zo ta zagi mahaifinsa da mahaifiyarsa kuma ta shaida masa ce “wallahi ba za mu ba ka gwamnati a Kano ba”.

Abba Kabir Yusuf ya yi zargin cewa ta sa an doki wani ma’aikacin DSS wanda ya zo yana daukar hoto a lokacin da lamarin yake faruwa.

Gwamnan na Kano ya kuma ce matar shugaban DSS din ta hana shi shiga jirgin sama inda ta sa jami’an tsaron da ke mata rakiya su kama shi.

Wannan lamari dai ya jawo ce-ce-ku-ce matuka a watan Janairu inda aka yi ta muhawara a kansa a kafafen watsa labarai da na sada zumunta.

Har yanzu Aisha Bichi ba ta ce komai kan wannan lamari ba amma danta Abba Yusuf Bichi bayan faruwar lamarin ya wallafa sako a shafin Twitter inda ya ce mahaifiyarsa ba ta bayar da umarnin a kama Abba Gida-Gida ba ko kashe wani dan siyasa.

Haka ka hukumar DSS ta fitar da sanarwa jim kadan bayan faruwar lamarin inda ta yi zargin cewa akwai wasu ‘yan siyasa a ciki da wajen gwamnati da ke kokarin daukar nauyin bata sunan shugaban DSS Yusuf Magaji Bichi.

DSS ta yi zargin cewa masu hannu a wannan lamarin sun hada kai da kungiyoyi masu zaman kansu domin shirya tattaki da zanga-zanga kan titi da taron manema labarai domin bata sunan Yusuf Bichi da iyalansa.

TRT Afrika