Janar-Janar din da ke fada da juna a Sudan sun amince su aika wakilai don sasantawa, mai yiwuwa a Saudiyya, in ji wani babban jami’in Majalisar Dinkin Duniya.
Idan har aka samu damar tattaunawar, za su mayar da hankai ne a kan yadda za a tsagaita wuta mai dorewa da masu sa ido na cikin gida da kasashen waje za su lura da ita, kamar yadda Volker Perthes ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AP a ranar Litinin.
Ya kuma yi gargadin cewa har yanzu akwai kalubale wajen aiwatar da tattaunawar.
A makon da ya wuce an cimma yarjejeniyar tsagaita wuta ta wucin gadi amma a wasu yankunan kawai ta yi aiki, inda aka ci gaba da gumurzu tare da raba fararen hula da muhallansu a wasu wuraren.
Kungiyoyin agaji suna ta kokarin taimakon mutane a kasar da kusan kashi uku cikin hudu na yawan al’ummarta miliyan 46 suka dogara da ayyukan agajin kasashen waje.
Hukumar Abinci ta MDD a ranar Litinin ta ce za ta ci gaba da aiwatar da ayyukanta a Sudan. A baya ta dakatar da ayyukan nata ne saboda kashe mambobinta uku da aka yi a yankin Darfur tun farkon fara rikicin.
Shugabar hukumar Cindy McCain a wata sanarwa ta ce za a fara rabon kayan agajin a yankunan al-Qadaref da Gezira da Kassala da kuma White Nile idan har an samu sararin yin hakan.
Masifun da yakin ya jawo zuwa yanzu
Ma’aikatar Lafiya ta kasar ta ce an kashe mutum 528 zuwa yanzu, sannan mutum 4,599 ne suka jikkata a yakin da aka fara tun ranar 15 ga watan Afrilu.
Ma’aikatar Lafiyar ta ce ana rikicin ne a jihohi 12 cikin 18 na kasar.
Sannan rikicin ya raba kusan mutum 75,000 da muhallansu a birnin Khartoum da jihohin Blue Nile da Arewacin Kordofan da kuma yankin Darfur, in ji MDD.