Hare-haren sama da ruwan bama-bamai da luguden wuta. Ƙarancin abinci da magunguna. Fiye da mutum 12,000 sun mutu. Ɗaruruwan mutane sun rasa muhallansu.
Ana ci gaba da tafka mummunan yaƙin da aka fara tun wata tara da suka wuce, tsakanin janar ɗin soji biyu na Sudan, lamarin da ya ta'azzara abin da Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana a matsayin rikicin da ya fi raba mutane da muhalkansu a duniya tare da tunkuɗa ƙasa ta uku mafi girma a Afirka a cikin masifa.
A cewar wani ɗan sa kai a wani ɗakin ba da agajin gaggawa a Bahri, wani birni da yake arewa da birnin Khartoum, kayan abincin da ke kantuna da wuraren ajiya a yankin suna ta ƙarewa.
Monzer O. mai sana'ar nazari kan harkokin kudade ne. Amma yakin basasar Sudan - wanda dakarun sojin kaar karkashin Abdel Fattah al Burhan (SAF) suke yakar mayakan RSF da Mohamed Hamdan Daglo ke wa jagoranci - ya janyo dakatar da wannan aiki da yake yi koyaushe.
A yanzu, matashin mai shekara 32 ya sadaukar da kansa ga wata cibiyar bayar da taimakon gaggawa, yana rarraba abinci ta hanyar "takkyah" ko dakin dafa miya malakar gwamnati, da ma wasu ayyukan alheri ga jama'ar yankin. a yayin da yaki ya hana shigar da kayan abinci a yankunan.
A yanzu ana sayar da kilo din tumatur daya kan Fan din Sudan 9,000, kusan dalar Amurka $13. Monzer ya kuma bayyana cewa rikicin na nufin ana takura wa mazauna yankunan da rikicin ya shafa diban ruwa daga kogin Nil don sha, wanko da girke-girke.
"Yanayin ya munana matuka, kuma ba za mu iya tunkarar wannan matsalar mu kadai ba," in ji Monzer. "Dole a samar da yankunan zaman lafiya ta yadda kungiyoyi za su samu damar unguwanni su bayar da taimakon gaggawa."
Rikicin raba mutane da matsugunansu
Monzer ya kara da cewa "Mutane na iya kai komo a unguwa duk da wahalar yin hakan, kuma an sani cewar yankin Bahri na karkashin ikon mayakan RSF, saboda haka ba a iya tafiya a yankin sai an samu rubutaccen sakon izini daga kwamandan yankin."
Mafi yawan 'yan Sudan sun gudu daga gidajensu, zuwa wasu jihohin kasar ko kasashe makwabta irin su Chadi, don gujewa fadawa tarkon musayar wuta tsakanin mayakan SAF da RSF.
Wasu kuma dole ce ta sanya su suka zauna suka kasa barin yankunansu, saboda ko dai suna kula da dattawansu, marasa lafiyansu, suna da nakasa da wani dalilin rayuwa da ba zai iya ba su damar barin gida ba, wasu kuma kawai suna ganin ba zai yiwu su bar gidajensu su je suna neman mafaka a wasu wuraren ba.
A yayin da mafi yawan iyalai suka bar yankunan don neman salama, Monzer ya zauna a yankin saboda taimakon dattijo a gidansu da yake taimakawa da abinci, sannan a gidan nasa akwai kuma wata yarinya da ke da nakasa.
Tun bayan rikici ya barke a ranar 15 ga watan Afrilun 2023, an raba sama da mutane miliyan 7.3 da matsugunansu, wanda ya sanya kasar ta zama mafi yawan nakasassu a duniya, kamar yadda Ofishin Kula da 'Yan Gudun Hijira na Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana (OCHA) ya bayyana.
Sakatare Janar na Kungiyar Likitocin Komai da Ruwanka Chris Lockyear ya shaida wa TRT World cewa "Muna ganin mutane na tsallaka kan iyaka suna guduwa zuwa Chadi, a yayin da suka je Chadin, misali sai su samu babu wani tallafin jinkai na a zo a gani daga hukumomin jinkai da jama'ar yankunan da suka je."
"Wannan bangare da dukkan mu muke kira da a bayar da karin taimako ga mutanen da suke guje wa rikicin Sudan - bukatun suna da yawa, amma ba mu da karfin da za mu magance su gaba daya," in ji Lockyear, yana mai kara wa da cewar wahalar da ake sha wajen kawo magunguna na taka rawa sosai wajen shafar ayyukan jinkai na kungiyar likitocin.
Hana shigar da magunguna
Kusan mutum miliyan 25 na bukatar taimakon jinkai a Sudan...
A watan Satumban 2023, an haramta shigar da magunguna zuwa Khartoum don kar a dinga yin magani ga sojojin RSF da ake jikkatawa a babban birnin, wanda hakan ya jefa rayuwar dubunnan daruruwan mutane cikin hatsari, musamman ma wadanda suke kwance a asibitoci, kamar yadda MSF suka sanar.
An rufe kusan dukkan asibitoci da wuraren sayar da magunguna a Khartoum, in ji Mohamed S, yana mai kara wa da cewa wadanda ke samun raunuka manya sai dai su bar babban birnin zuwa wasu garuruwan don neman lafiya.
"Baffana ya rasu watanni uku da suka gabata. Ya sha fama da ciwon koda," in ji Mohammed yayin tattauna wa da TRT World daga DOha, inda ya yi kusan dukkan rayuwarsa.
"Ya zamar masa wajibi ya tafi zuwa wata jihar don ya dinga yin wankin koda saboda an rufe dukkan asibitocin da ke kusa da Shambat, gundumar da yake zaune a Khartoum. An sha wahala kafin a samu motar ma da za ta dauke shi zuwa waje," in ji injiniyan mai shekara 33.
"A lokacin da ya isa wajen, nan take rai ya yi halin sa. Akwai dogon layi, mutane na ta jira, kuma injin wankin kodar ba ya aiki yadda ya kamata. Likitocin sun kasa yin katabus saboda halin da yake ciki yana kara munana sosai."
Kamar sauran 'yan kasar Sudan da ke rayuwa a kasashen waje, Mohamed na sauraron bayanai game da danginsa a ko yaushe, wanda mafi yawan su sun bar yankin Shambat.
Mohamed ya kuma ce karancin lantarki a kasar ya sake rura wutar yakin da ake yi, yana janyo katsewar lantarkin da katse hanyoyin sadarwar intanet.
A wasu lokutan a kan dauki mako guda ko biyu ba tare da samun hasken lantarki ba, madalla ga ayyukan 'yan sa kai da suke bugun kirji suke gyaran wutar lantarkin a duk lokacin da ta katse.
Tun 19 ga Disamban bara, sama da mutum 12,000 aka kashe a Sudan bayan barkewar rikicin. Sai dai kuma, wasu na ganin wannan adadi ya fi haka, an boye gaskiyar adadin wadanda aka kashe.
Kamar yadda Mohamed ya fada, "Ku dakatar da yakin, ta yadda mutane za su iya koma wa gidajensu su zauna lafiya."