Daga Mazhun Idris
Wannan shekarar ta kasance mai cike da gaurayen lamurra a fagen siyasar Afirka.
Daga cikin ƙasashe fiye da 12 da aka shirya gudanar da zaɓukan Shugaban Ƙasa tsakanin watannin Janairu da Disamban shekarar 2023, an gudanar da zaɓe a takwas daga cikinsu.
Sai dai kuma, sojoji sun hamɓare zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Gabon ba tare da ɓata lokaci ba, kuma Saliyo na fama da rikici ga kuma juyin mulkin da bai yi nasara ba.
Biyar daga cikinsu - Sudan da Sudan ta Kudu da Mali da Burkina Faso - ba su gudanar da zaɓukan ba ko sun ɗaga lokacin gudanar da su.
TRT ta yi waiwayen yadda ƙasashe Takwas ɗin suka gudanar da zaɓukan da kuma abin da ya biyo baya.
Nijeriya: Ga Raba Gardama
Jam'iyyu 18 ne suka tsayar da ƴan takara yayin da ƙasa mai bin tafarkin Dimokuraɗiyya mafi muhimmanci a Afrika ta shiga zaɓukanta da ake gudanarwa bayan shekaru huɗu, ranar 25 ga watan Fabrairu, domin zaɓar wanda zai gaji shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, wanda ya kammala wa'adin mulkinsa na biyu.
Bola Ahmed Tinubu na jam'iyya mai mulki ta APC ya lashe zaben, amma biyu daga cikin ƴan takarar manyan jam'iyyun hamayya uku - Atiku Abubakar na PDP da kuma Peter Obi na Labour Party - sun ƙalubalanci sakamakon zaɓen a kotu.
A ranar 29 ga watan Mayu, an rantsar da Tinubu a matsayin shugaban ƙasa, karo na huɗu da farar hula ya miƙa wa wani farar hular iko tun da Nijeriya ta dawo mulkin Dimokuraɗiyya a shekarar 1999. A ranar 26 ga watan Oktoba, Kotun Ƙoli ta tabbatar da nasararsa.
Saliyo: Rikicin Bayan Zaɓe
Ranar 24 ga watan Yuni, ƙasar ta Yammacin Afirka ta gudanar da zaɓuka a karo na biyar tun kawo ƙarshen yaƙin basasa a 2002
Shugaban ƙasa mai ci, Julius Maada Bio, ya samu kashi 56% na ƙuri'un da aka kaɗa, lamarin da ya sa ya lashe wa'adin shekara biyar ɗinsa na ƙarshe.
Samuel Kamara na jam'iyyar hamayya ta All People's Congress ne ya zo na biyu da kashi 41 cikin 100 na ƙuri'un.
A ranar 27 ga watan Yuni, hukumar zaɓe ta ƙasar ta tabbatar da nasarar Bio, wanda ya samu ƙarin kashi ɗaya tal a kan kashi 55% da ake buƙata, domin kauce wa tafiya zagaye na biyu. Amma Kamara ya yi watsi da sakamakon.
Sai dai, Saliyo na ta fama da rikicin siyasa tun watan Yuni, wanda ya tiƙe da wani juyin mulkin da bai yi nasara ba a watan Nuwamba.
Ƙungiyar Raya Tattalin Arziƙi Ƙasashen Yammacin Afirka ta ECOWAS tana goyon bayan Bio domin kare mulkin Dimokuraɗiyya.
Zimbabwe: Sauyi Alum-Salum
Ranar 23 ga watan Agusta, Zimbabwe ta gudanar da zaɓenta na ƙasa a karo na Biyu tun juyin mulkin da ya kawo ƙarshen mulki Robert Mugabe a 2017.
Shugaban ƙasa Emmerson Mnangagwa ya sake tsayawa takara bayan ya kammala wa'adin mulkinsa na farko.
Wanda ya tsaya takara ƙarƙashin inuwar ZANU-PF, jam'iyar da ta mulki ƙasar tun samun ƴancin kai a 1980, Mnangagwa ya lashe kashi 52.6 cikin 100 na ƙuri'un.
Ya kayar da abokin hamayyarsa Nelson Chamisa (wanda ya samu kashi kashi 44 cikin 100 na kuri'un).
Ranar 4 ga watan Satumba aka rantsar da Mnangagwa domin kama aiki.
Jam'iyyar Chamisa ta Citizens Coalition for Change ta yi watsi da zaɓen a matsayin "shirme", amma ba ta ƙalubalanci sakamakon a kotu ba.
Gabon: Bango Ya Tsage
Iyalan Bongo sun mulki wannan ƙasar Tsakiyar Afrika mai arziƙin tsawon shekaru 55. Ali Bongo, ɗan shugaba Omar Bongo, ya tsaya takara a zaɓen shugaban ƙasa ranar 26 ga watan Agusta kuma ya lashe da kashi 64 cikin 100 na ƙuri'un.
Amma sai abubuwa suka fara taɓarɓarewa a cikin ƴan sa'o'i. Gungun jami'an sojoji sun sanar a talabijin cewa sun karɓe mulki kuma sun yi wa Bongo ɗaurin talala.
Ranar 30 ga watan Agusta, an sanar da sunan Janar Brice Oligui Nguema a matsayin sabon shugaban mulkin soja na Gabon, duk da an yi Allah wadai sosai da juyin mulkin da ya ƙara a kan jerin juyin mulkin sojoji na baya bayan nan, da suka katse wa'adin mulkin zaɓaɓɓun gwamnatoci a ƙasashen Afrika masu yawa.
Ranar 13 ga watan Nuwamba, biyo bayan matsin lamba daga ƙasashen duniya, gwamnatin sojojin ta fitar da jadawalin miƙa mulki, wanda ya saka watan Agustan shekarar 2025 a matsayin lokacin gudanar da babban zaɓen.
An shirya za a ƙaddamar da zaben raba-gardama kan amincewa da sabon kundin tsarin mulkin ƙasa a kafin wannan lokacin.
Liberia: Mashahurin mutum ya sauka
Ranar 10 ga watan Oktoba, Laberiya ta gudanar da zaɓe yayin da shugaban ƙasa mai ci, George Weah, ya nemi wa'adi na biyu na shekaru shida.
Tsohon tauraron ƙwallon ƙafar ya wuce kan gaba a zagaye na farko amma ya gaza samun adadin ƙuri'un da ake buƙata a samu nasara kai-tsaye.
Zagaye na Biyu na Zaɓen na ranar 14 ga watan Nuwamba ya haɗa shugaban ƙasa mai ci da babban abokin hamayyarsa, Joseph Boakai, tsohon mataimakin shugaban ƙasa.
A wata ishara ta nuna tagomashinsa na Dimokuraɗiyya, Weah ya amince da shan kaye, bayan an ce Boakai ne ya lashe zagaye na biyun da aka yi kare jini biri jini.
Madagascar: Ƙauracewa da rashin fitowa zaɓe sosai
Ƙasar da ke kan tsibiri ta gudanar da zaɓe ranar 16 ga watan Nuwamba domin zaɓa tsakanin shugaban ƙasa mai ci, Andry Rajoelina (Shekaru 49) da sauran ƴan takarar a zaɓen da yawancin jam'iyyun hamayya suka ƙaurace wa.
Adadin waɗanda suka fito zaɓen shi ne kashi 46.35 cikin 100, adadi mafi ƙaranci a tarihinta.
Rejoelina ya samu kashi 58.96 cikin 100 na ƙuri'un kuma ya kayar da ƴan takara goma sha biyu, 10 daga cikinsu sun ƙaurace wa zaɓen, duk da an saka sunayensu a kan takardun zaɓen.
Ranar 1 ga watan Disamba, Babbar Kotun Tsarin Mulkin ta yi watsi da ƙorafe-ƙorafe dabam-daban a kan sakamakon zaɓen na farko, sannan ta tabbatar da wa'adin Shugabancin ƙasa na Rojoelina karo na uku.
Masar: el-Sisi zai yi Ƙwar-uku?
Ranar 1 ga watan Disamba, an buɗe rumfunan zaɓe a ƙasashe 121 domin mazauna waje su yi zaɓe a zaɓen shugaban ƙasa, wanda daga bisani aka gudanar a Masar tsakanin ranakun 10 zuwa 12 ga watan Disamba.
Shugaban ƙasa Abdel Fattah el-Sisi ne ya sake zarcewa a karo na yuku bayan ya samu kashi 89.6 cikin 100 na ƙuri'un da aka kada a zaben da kashi 66.8 na wadanda suka yi rijista suka kada kuri'u.
el-Sisi ya kayar da 'yan hamayya Farid Zahran, da Abdel Sábado Yamama da kuma Hazem Omar, a sakamakon da hukumar zabe ta sanar.
DR Congo: Wanda ya taɓa lashe kyautar zaman lafiya ya bi sahu
Yayin da suke zama cikamakin zaɓuɓɓukan shugaban ƙasa a shekarar 2023 a nahiyar, al'ummar ƙasa ta Huɗu mafi yawan jama'a a Afrika, za su kaɗa ƙuri'unsu ranar 20 ga watan Disamba.
Shugaba mai ci, Felix Tshisekedi (Shekaru 60) yana neman a zaɓe shi na wani wa'adin.
A cikin ƴan takarar jam'iyun hamayya guda 24 da ke ƙoƙarin kayar da Tshisekedi akwai Dr Denis Mukwege, wanda ya lashe kyautar zaman lafiya kuma fitaccen likitan mata.