Fasinjojin jirgin sun shiga rudani bayan sun ga kansu a Asaba maimakon Abuja. / Hoto: Dawisu/X

Kamfanin jirgin sama na United Nigeria ya yi karin haske bayan jirgin kamfanin da zai je Abuja ya sauka a birnin Asaba na jihar Delta a ranar Lahadi, lamarin da ya yi matukar tayar da kura a shafukan sada zumunta.

Tun da farko wasu daga cikin fasinjojin jirgin sun yi rubutu a shafukan sada zumunta inda suka bayyana cewa sun taso daga Legas za su je Abuja, bayan sun isa sai ma’aikatan jirgin suka yi sanarwa cewa sun isa Abuja, amma daga baya sai suka lura kan cewa a Asaba jirgin ya sauka.

Wannan lamarin ya yi matukar jawo ce-ce-ku-ce inda jama’a suka yi ta bayyana mabambanta ra’ayoyi kan dalilin da suke ganin ya jawo faruwar wannan lamari.

Sai dai a wata sanarwa da kamfanin jirgin saman na United Nigeria ya fitar a shafukansa na sada zumunta, ya bayyana cewa matsalar yanayi aka samu abin da ya sa jirgin ya juya zuwa Asaba.

Haka kuma kamfanin ya ce masu sanarwa na cikin jirgin su suka kara ruda fasinjojin jirgin.

“Sakamakon rashin kyawun yanayi, an sauya wa jirgin United Nigeria mai lamba NUA 0505 hanya wanda ya taso daga MM2 Legas zai je Abuja a ranar Lahadi, 26 ga watan Nuwamba,” in ji sanarwar.

“A lokacin, an sanar da direban jirgin dalla-dalla sauyin hanya ta wucin-gadi da aka yi.

“Sai dai masu sanarwa sun yi sanarwa ba daidai ba a lokacin da jirgin ya isa Asaba, lamarin da ya jawo rudani a fasinjojin,” kamar yadda sanarwar da kara da cewa.

Kamfanin kuma ya tabbatar da cewa jirgin daga baya ya isa Abuja lafiya.

TRT Afrika