Nijar ta sha alwashin kare 'yancinta na zama ƙasar mai cin gashin kanta./Hoto: AFP

Ukraine ta ce zargin da Nijar ta yi mata na goyon bayan ta'addanci a yankin Sahel "ba shi da tushe kuma ba gaskiya ba ne,” a yayin da ƙasar ta yammacin Afirka ta yanke hulɗar jakadanci da Kyiv bisa zargin goyon bayan "ƙungiyoyin 'yan ta'adda" a Mali.

“Zarge-zargen da wakilin wannan ƙasar (Nija) ta yi wa Ukraine ba su da tushe kuma ba gaskiya ba ne,” a cewar wata sanarwa da Ma'aikatar Harkokin Wajen Ukraine ta fitar ranar Alhamis.

Sanarwar ta ce Ukraine tana sace cewa Nijar na da 'yancin yanke hulɗar diflomasiyya da ita, sai dai ta yi watsi da zarge-zargen da ake yi wa ƙasar na "goyon bayan ta'addanci a duniya,” da kuma “keta dokokin Majalisar Ɗinkin Duniya da na ƙasashen duniya."

Ukraine ta ce tana ɗaukar matakin a matsayin “nuna goyon baya" ga Rasha, wadda take zargi da goyon bayan “tarzoma da fito-na-fito” a faɗin duniya, ciki har da ƙasashen Afirka.

'Babu hujja'

“Abin takaici ne yadda hukumomi a Nijar suka yanke hulɗar jakadanci da Ukraine ba tare da yin bincike ba kan abin da ya faru a Mali kuma ba tare da bayar da wata hujja da ke nuna cewa mun aikata laifin da ake zarginmu da shi ba," in ji sanarwar.

Ta ƙara da cewa Ukraine za ta ci gaba da ƙoƙarin yauƙaƙa dangantaka da ƙasashen Afirka bisa wasu manufofi da suka haɗa da rashin tsoma baki a harkokin cikin gida na ƙasashen, da mumunta 'yancinsu na kasancewa ƙasashe masu gashin kansu da kuma muradun da Majalisar Ɗinkin Duniya ta tsara.

Ranar Talata Nijar ta sanar da yanke hulɗar jakadanci da Ukraine "nan-take" bayan ta zarge ta da goyon bayan "ƙungiyoyin 'yan ta'adda" a Mali sannan ta ce za ta kai ta gaban Majalisar Ɗinkin Duniya domin a ladabtar da ita.

Ta ɗauki matakin ne kwana biyu bayan Mali ta sanar da yanke alaƙa da Ukraine bisa zarginta da goyon bayan 'yan ta'adda waɗanda suka kashe sojojinta yayin wani gumurzu a kusa da kan iyakarta da Algeria a watan jiya.

AA